Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).
Bayan haka, lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), mafi kyawun shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu (Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkira a cikin addini, kuma duk abin da aka kirkira a cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya tsare mu daga gare ta, amin.
Sannan bayan haka, a makon da jiya mun ga abin da Alkur’ani da Hadisi suka fada game da wajibcin yin azumi ga wadanda sharuddan gudanar da shi suka hau kansu da kuma haduwar al’ummar Musulmi kan tilascin yin azumin da matsayin wanda ya yi inkarin wajibcinsa.
Sannan mun ga bayani kan wasu daga cikin falala da hikimomin da ke ciki azumin watan Ramadan. Yau, cikin yardar Allah, ga ci gaba:
11. Daga cikin abin da addinin Musulunci ya bayyana game da matsayin azumi akwai jerawar da ake yi wa masu azumi cikin wadanda Allah Ya yi wa tattalin wata gafara da lada mai girma, kamar yadda bayanin haka ya zo a surar Ahzab, aya ta 35. Shi ya sa ma a surar Bakara, aya ta 184, Allah Ya nuna a yi azumin alheri ne “… in kun kasance kuna sani.”
12. Lallai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayyana a cikin hadisai tabbatattu, cewa azumi makangi ne daga sha’awoyi kuma garkuwa ne daga wuta. Sannan Allah, Wanda albarkar sunanSa ta daukaka, ya kebance azumi da wata kofa a Aljanna, wadda aka yi wa suna Rayyan.
Dalilin kasancewar azumi makangin sha’awa kuwa shi ne yayin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi kira ga matasa cewa duk wanda yake da ikon ya yi aure, to ya yi, domin shi ne mafi sanyawar runtse idanu daga kalle-kallen haram, kuma mafi tsaron farji daga zina; in ba ya da ikon yin auren kuwa, to ya yi azumi, “saboda shi dandaka ne.” Ma’ana mai yanke sha’awar jima’i ne. Buhari, mujalladi na 4, shafi na 106; da Muslim, Hadisi na 1,400, suka ruwaito shi daga Abdullahi Ibn Mas’ud (Allah Ya yarda da shi).
Wannan kuwa haka yake domin azumi yana rage karfin gabbai, ya dabaibaye su daga guje-gujen zuwa wurin sha’awa, ya natsar da su, su yi lif, ya sanya musu linzami. Haka nan ya tabbata cewa azumi yana da tasiri mai ban mamaki wajen tsare gabban bayyane da wani karfi na boye – tsoron Allah. Allah Shi ne Mafi sani!
Dalilin kasancewar azumi garkuwa daga wuta kuwa shi ne lallai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bayyana cewa Aljanna, an lullube ta da abubuwan ki, kamar na wahalhalu, amma ita wuta, an lullube ta da abubuwan ban sha’awa, kamar na morewar duniya. Saboda haka idan Musulmi ya gane cewa azumi yana hana wa sha’awa sakat, ya karya mata lago, alhali ita ke kai mutum zuwa ga wuta, zai gane cewa ke nan azumi ya kange shi daga gare ta, kuma Aljanna tana jan shi zuwa gare ta, ya nisanci wutar.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Ba wani daga cikin bayin Allah da zai azumci wata rana saboda Allah, face Allah Ya nesanta shi daga wuta shekara saba’in.” Buhari, mujalladi na 6, shafi na 35 da Muslim, Hadisi na 1,153, suka ruwaito shi daga Abu Sa’idil Khudriy (Allah Ya yarda da shi).
Haka nan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Azumi garkuwa ne, wanda bawan Allah yake amfani da ita don kange kansa daga wuta.” Imam Ahmad, mujalladi na 3, shafi na 241 da 297 ya ruwaito shi daga Jabir (Allah Ya yarda da shi); sai kuma a mujalladi na 4, shafi na 22 daga Usman bn Abu Al’as (Allah Ya yarda da shi).
Har wa yau Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya azumci rana daya saboda Allah, Allah Zai sanya gwalalo (ramin da ake yi a bayan ganuwar tsaron gari a da) tsakaninsa da wuta kamar nisan da ke tsakanin sama da kasa (wato nisan tafiya shekara dari biyar, kamar yadda ya zo a wani Hadisin).” Imamu Tirmiziy, Hadisi na 1,624, ya ruwaito shi daga Abu Umama (Allah Ya yarda da shi); dabaraniy ma ya fitar da shi a cikin littafin Alkabir, mujalladi na 8, shafi na 260 da 274 da 280; haka nan ya fitar da shi a cikin littafin Assaghir, mujalladi na 1, shafi na 273 daga Abu Addarda’u (Allah Ya yarda da shi).
13. Azumi yana shigar da mai yinsa Aljanna, musamman tunda yana nisantar da shi daga wuta a dalilin kular da yake yi da abin da azumin ya kunsa. Abu Umama (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Na ce ya Manzon Allah, ka shiryar da ni (ka nuna mini) wani aiki da zan aikata da zai shigar da ni Aljanna.” Sai ya ce, “Na hore ka da yin azumi, domin babu kamarsa.” Annasa’iy, mujalladi na 4, shafi na 165 da Ibnu Hibban, shafi na 232, a littafin Mawarid da Alhakim, mujalladi na 1, shafi na 421, suka ruwaito shi da isnadi ingantacce.
14. Mai azumi yana tare da farin ciki iri biyu: Lokacin da ya sha ruwa (buda-baki) da lokacin da ya hadu da Mahaliccinsa a ba shi sakamakon aikinsa domin Allah Ya ce Shi ne zai yi sakamakon azumin da kanSa.
15. Wari ko hamami ko bashin bakin mai azumi a wurin Allah, ya fi turaren miski kamshi. Wannan kuwa babban matsayi ne na azumi.
Duk wadannan darajoji na 14 da 15 suna cikin Hadisin da aka samo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), inda ya ce, “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Dukkan aikin (ibadar) dan Adam nasa ne, sai dai azumi, wanda shi Nawa ne, Ni ne zan ba da sakamakonsa’ …. Na rantse da Wanda ran Muhammadu ke hannunSa, warin bakin mai azumi a wurin Allah, ya fi turaren miski kamshi. Mai azumi yana da farin ciki biyu: Idan ya yi buda-baki, ya yi farin ciki; kuma idan ya hadu da Ubangijinsa, ya yi farin ciki da azuminsa.” Buhari, mujalladi na 4, shafi na 88 da Muslim, Hadisi na 1,151, suka ruwaito shi.
A riwayar Buhari: “Allah Yana cewa, “(mai azumi) ya bar cinsa da shansa da sha’awarsa saboda Ni, saboda haka azumi Nawa ne kuma Ni ne zan ba da sakamakonsa alhalin kowane kyakkyawan aiki yana da sakamako goma kwatankwacinsa.”
Duk wannan ana magana ne a kan azumi kowane iri, to, yaya matsayin na farilla? Allah Ya sa mu dace.
Bari mu dakata a nan, sai mako na gaba, mu ci gaba, in Allah Ya kai mu. Allah Ya sa mu bude-baki lafiya kuma Ya karba mana, amin!
Wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuh!