✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsanancin karancin abinci zai ta’azzara mutuwar kananan yara a Gaza – MDD

Kashi 90 na kananan yara daga shekara 5 zuwa kasa a Gaza sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, matsanancin karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki da ta’azzarar cutuka na iya haifar da karuwar mutuwar kananan yara a Zirin Gaza.

Mako 20 da fara wannan yaki tsakanin Isra’ila da Hamas a yankin Zirin Gaza, Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedin cewa, akwai matsanancin karancin abinci da tsaftataccen ruwa a yankin na Falasdinawa, inda suka kara da cewa akasarin kananan yara sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Mataimakin Shugaban Ayyukan jin-kai na Assusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Ted Chaiban ya ce, Zirin Gaza zai fuskanci mutuwar kananan yara, wanda zai ta’azzara halin da ake ciki a yanzu.

Wani nazari na hadin gwiwa da Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka yi na nuni da cewa, kashi 90 na kananan yara daga shekara 5 zuwa kasa a Gaza sun kamu da cutuka masu yaduwa.

Kashi 70 na kananan yaran sun yi fama da cutar amai da gudawa gabanin wannan nazari, abin da ke nuni da karin har ninki 23 idan aka kwatanta da 2022, kamar yadda BBK ya ruwaito.

Harin da mayakan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum dubu 1 da 160 ne ya haddasa yakin Gaza Mahukuntan Zirin Gaza sun ce, hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin ya yi sanadiyar mutuwar mutum dubu 29 a halin da ake ciki.

Tun da aka fara wannan yakin, Zirin Gaza ya fada cikin matsalar karancin abinci mai gina jiki, sakamakon yadda aka takaita shiga.