✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin rayuwa: Mu koma ga Allah – Sarkin Ningi

Mai martaba sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad danyaya ya bayyana cewa yaki da hukumomin tsaro suke yi da kungiyar Boko Haram sama da shekara bakwai,…

Mai martaba sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad danyaya ya bayyana cewa yaki da hukumomin tsaro suke yi da kungiyar Boko Haram sama da shekara bakwai, har yanzu da sauran rina a kaba, sakamakon irin jabawan da ya ce yake samu daga masana zamantakewar al’umma.

Ya bayyan haka ne lokacin da Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kai masa ziyara a fadarsa, a lokacin da aka gabatar da wa’azin kasa a kwanakin baya.
“Amma tabbas sojojin Najeriya sun yi kokari sosai a yayin da suke ci gaba da fafatawa da ’yan kungiyar ta Boko Haram, domin zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne manyan sinadarin da ke kawo ci gaba cikin hanzari a kowace kasa ta duniya,” inji shi.
Sarkin ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa kasar nan tana bukatar addu’o’i, sakamakon matsalolin tsadar rayuwa da ake ci gaba da fuskanta a sassa daban-daban na kasar nan da suka hada da talauci da satar mutane da suka zamo ruwan dare.
Ya bukaci malaman addinai da su rika rage gaba a wa’azozin da suke gabatarwa, domin watakila ta haka za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma. Ya ce kowa ya san malamai magada annabawa ne, dole sai kowa ya yi hakuri da dan uwansa kafin a samu ci gaba a kasar nan.
Daga karshe, ya yi amfani da wannan dama, inda ya bukaci al’umma su ci gaba da addu’a, Allah zai kawo karshen matsalar talauci da tsadar kayan abinci da ake fuskanta. “Babu abin da ya fi karfin addu’a a wajen Allah,” inji sarkin na Ningi.