✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalolin da ke fuskantar ’yan gudun hijira don Boko Haram

A kwanakin baya ne sojoji suka kai farmaki tare da bude wuta a wani mazaunin wasu ’yan gudun hijira da suka gudo daga garuruwansu na…

A kwanakin baya ne sojoji suka kai farmaki tare da bude wuta a wani mazaunin wasu ’yan gudun hijira da suka gudo daga garuruwansu na aihani a Arewa-maso gabashin Najeriya saboda ta’addancin ’yan Boko Haram. A farmakin da sojan suka kai a mazaunin nasu da ke cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja, akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu. Da asubahi ne sojojin tare da rakiyar wasu jami’an tsaron na daban suka kai farmaki sansanin da ke unguwar Durumi da ke Abuja, inda mafi yawan mutanen da ke wurin ’yan gudun hijira ne da suka gudo daga karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno, a sakamakon mamaye garin nasu da ’yan Boko Haram suka yi, kodayake har yanzu ba a samu tabbaci ba cewa ko Hukumar Agajin Gaugawa (NEMA) ta tabbatar da amincewa wurin na ’yan gudun hijira ne ko akasin haka.

daya daga cikin mazauna unguwar da ya samu rauni sakamakon farmakin, Ishaku Amos ya ce jami’an tsaron sun far wa gidajensu ne a yayin da suke barci, inda suka yi ta harbi kuma suna kama mutanen da suka yi kokarin tserewa. Amos, wanda ke sana’ar tuka motar Kekenapep, ya ce yana barci ne a cikin baca, a yayin da ya ji karar harbe-harbe. Ya ce yana cikin mutane 146 da aka kama, aka tafi da su Barikin Lungi da ke Asokoro, inda aka yi musu tambayoyi. Kamar yadda ya kara bayani, ya ce mutum 109 aka saki wanshekare, sauran kuma aka ci gaba da tsare su domin ci gaba da bincike. Amos ya ce an tambayi sunayensu da sana’arsu da kuma cewa tswon wane lokaci ne suke zaune a unguwar (kauyen).
Babu takamaimai bayanin abin da ya sanya sojojin suka kai wannan farmakin, wanda irinsa ya taba faruwa a baya a unguwar Apo, Abuja, inda wasu jami’an bincike na farin kaya (SSS) suka bude wa wasu leburori da masu neman aikin karfi da ke kwana a kangon wani gida wuta; inda har mutum bakwai suka rasa rayukansu. Jami’an tsaron, a lokacin sai suka ce ai mutanen ’yan Boko Haram ne.
A wannan farmakin na kwanan nan, mutanen da aka farmaka sun gudo ne daga Gwoza saboda tsoron ta’addacin ’yan Boko Haram, sai ga shi sun yi gudun gara sun fada gidan zago, inda suka gamu da irin abin tsoron da ya sanya su gudun hijira a hannun jami’an tsaro. daya daga cikin shugabannin mutanen mai suna Zubairu Muhmmad ya ce abin da aka yi masu rashin adalci ne, musamman kuma ga shi mutanen ma’aikata ne da ke leburanci ko kabu-kabu da sauran ayyukan karfi.
Shi kuwa da yake maida martani game da faruwar al’amarin, jami’in hulda da jama’a na Rundunar Sojan Najeriya, Birgediya-Janar Olajide Laleye, ya ce tabbas akwai bayanan sirri da suka tabbatar da cewa akwai wasu ’yan ta’adda da suka tsero daga Gwoza, suka yada zango a wani sashi na Abuja. Ya tabbatar da cewa lallai sojoji sun kai farmakin aiki a unguwar da ake batu, sai dai ya ce mazauna unguwar ne suka fara bude musu wuta a lokacin da suke kan aikin bincike. Laleye kuma ya musanta cewa mutum uku ne suka mutu, ya ce mutum biyu suka mutu a sakamakon farmakin.
A Satumbar bara ma, mutane bakwai, wadanda leburori ne da masu sana’ar tuka Kekenapep da suka fito daga Arewacin kasar nan suka mutu a yayin da jami’an hukumar bincike ta farin kaya (SSS) suka kai irin wannan farmaki a unguwar Apo-Abuja, mazaunin ’yan majalisar wakilai ta tarayya. Hukumar Kula Da Hakkin dan Adam Ta kasa ta kai batun nan kotu, ta tuhumi jami’an SSS da kisan mutane ba da hakki ba, inda kuma kotu ta yanke hukuncin da ya tabbatar da laifin jami’an. Ita ma kungiyar Kare Hakkin Al’umma (Cibil Rights Congress) ta bayyana wannan farmaki na baya-bayan nan da cewa iri daya ne da wanda ya faru a bara.
Al’amarin yana da daure kai yadda duk da korafin da al’umma suka dade suna yi amma sojoji za su kai farmaki sansanin da farar hula ke zaune ba tare da sun samu cikakken tabbacin akwai masu laifi a wurin ba. Musamman kuma suka ki daukar darasi daga irin wannan kuskure da suka aikata a bara. Hasali ma, koda an samu tabbacin mazauna unguwar na aikata wani laifi, wannan bai isa dalilin da za a dauki irin wannan mataki na bude musu wuta ba kai tsaye, sannan daga baya a ce za a gudanar da bincike.
Mu dai a ganinmu, har yanzu ba a dauki darasi ba daga abin da ya faru a bara, don haka lallai ya kamata hukumar da ta dace da Majalisar Tarayya su gudanar da cikakken bincike kan al’amarin. Koma dai yaya al’amarin yake, ya kamata jami’an tsaro su rika gudanar da aikinsu bisa doka. Don haka, a wannan badakala, ya akmata a hukunta duk wani jami’i da aka samu da hannun ya wuce makadi da rawa.