Haqiqa Najeriya qasa ce da Allah Yake son ta amma mutanen cikinta suna ganganci da rayuwarsu ta wajen kashe qasa da yi mata zagon qasa, wanda tarihi ya nuna tun wajen shekaru 52 da suka shige qasar nan ta shiga wasu rigingimu na yaqin basasa da kashe-kashe irin na qabilanci da bangaranci, daga baya aka shiga fama da rikicin addini irin su na Maitatsine da kuma rikicin Musulmi da Kirista a wasu sassan qasar nan. Sannan na ga baya-bayan shi ne rikicin boko haram da na fadace-fadacen Fulani da makiyaya ko kashe-kashe na babu gaira, babu dalili. Ga satar mutane domin karbar kudin fansa ga kuma yadda kashe mutane ana yin tsafe-tsafe. Sannan wasu laifukan da suka yi wa qasar nan katutu sun hada da sace-sace da fashi da makami da fyade da zamba cikin aminci da yin algus da zalunci da yin sama da fadi koyin tsafe-tsafe, sannan wasu laifikan da suka zamo ruwan dare irinsu sace-sace da fashi da makami da kashin dankali, wato na sama ke danne na qasa da hassada da ganin qyashi da munafunci da hadamar mulki da neman tara dukiya ko ta halin qaqa.
Yanzu ban da Allah Yana son qasar nan, tana irin wadannan miyagun matsalolin ta ina za a samu ci gaba? Ai da tuni qasar nan ta wargaje kowa ya kama gabansa, ko kuma maqwabtan qasar nan su yi ta tara ’yan gudun hijira daga qasar nan a bar kasar babu kowa.
Lallai yana da kyau al’ummar qasar nan kowa ya shiga taitayinsa, a sa kishin qasar nan a gaba domin ciyar da ita gaba. Ko ba komai akwai ’yan baya masu tasowa.
Sannan wata shawara da zan zan bai wa ’yan siyasa masu son tsaya wa takara shi ne ya sa suke son lallai sai sun tsaya takara? Kwadayin arziki ko dukiyar da ake samu cikin sauqi ne ko kuma don su kece raini ko tsere wa sa’a?
Lallai su tsaya su yi tunanai, ga zabe nan yana tafe, qasa ta fara daukar dumi.
Wadanda damarsu bai isa su tsaya takara ba, sai a yi amfani da su wajen cin mutuncin masu mutunci a kafofin yada labarai ko a fili. a bawa wasu kayan maye su yi banga ana ba su kudin da ba su taka kara sun karya ba. An ya za a samu ci gaba a qasar nan kuwa?
Su kuma talakawa masu zabe, an kwadaita musu ’yan kudin da ba za su share musu hawaye na kwana uku ba. Kuma lallai al’umma su yi wani tsari na yadda za su koyi kiranye ga zababbun da suka zaba ba su kulawa da su, wannan shi ma abu ne mai muhimmanci amma wani abin haushi, sai ka ga wasu ’yan tumasanci suna zaune suna karbo wani abu daga wajen ’yan siyasa, kuma suna kare su, suna yi musu yaqi, lallai a yi hankali da irin wadannan al’umma domin an ce zomo ba ya fushi da makashinsa, sai maratayi.
Haqiqa irin wadannan al’umma masu kare ’yan siyasa ko shugabanni a kan irin zaluncin da suke yi, saboda suna karbar wani abu, sun fi kowa barna, domin da su ake rusa qasa.
Ina ma a ce ba kowa ne yakamata ya tsaya takara ba sai an tabbatar da ingancinsa da kishin qasa da son taimakon mutane, da ilmin shugabanci yana kuma da sana’a ko aikin yi ba kuma azzalumi ko dan kama karya ba, lallai da an fi haka ci gaba a qasar nan.
Haqiqa dukiya da matsayi su ne adon wannan zamani da muke ciki, amma sai an hada da adalci, gaskiya da tsoron Allah, sannan abin zai fi kwarjini sosai.
Masu yaqar hakan ko yin zagon qasa ga masu irin wannan kyawawan halaye na ci gaban qasa, to su ma a yaqe su kamar yadda za a yaqi ’yan tada zaune tsaye, ko da hukuma ta kawar da kai a kansu, to al’umma su dauki nauyin yaqi da su ta fuskar qyama da janye jiki da su.
A bangaren hukumar zabe kuwa kada ta kasa yin tsarin da ya kamata har ya kai ga lalacewar tsarin, musamman rashin kayan aiki, jami’an tsaro ko bata lokaci.
Shi kuma shugaban qasa Muhammad Buhari babban aikin da ke gabansa shi ne ya yi qoqari ya taimaka wajen nuna wa talakawa mutanen da yake ganin lallai abokan aiki ne irin sa, ma’ana suna kamanta gaskiya da riqon amana da biyayya a shugabancinsu, da ba da shawarar lallai a sake zabarsu su dawo, wadanda suke bata tsari ko ’yan son zuciya su ma ya fito qarara ya yi wa talakawa masu zabe bayaninsu daya bayan daya, da irin matsalar da suke haddasawa wajen hana shugabancinsa armashi kuma ya gaya wa al’umma kada a sake zabarsu tun daga kan gwamnoni zuwa ’yan majalisar tarayya da wakilai da ta dattijai.
Haka gwamnoni ma su fito su yi wa al’umma bayanin irin mutane da za’a zaba masu kishin qasa da hana wa a zabi wadanda ba su tabuka komai ba, sai yaudara da hana kawo cigaba.
In dai za ayi wannan gaskiya da gaskiya to shugaban qasa ya fita ko ba sabulu. Amma in ya yi shiru da nufin wai dimokuradiyya ta yi aikin kanta to gaskiya za a koma ’yar gidan jiya. Wannan shi ne bashin da talakawa suke bin shugaban kasa, domin kowa ya san babu wanda ya fi shugaban qasa samun rahotannin duk wani jami’in gwamnati da ma duk wasu al’umma (security report), saboda haka zai san duk irin wainar da ake toyawa a qasa baki daya, haka gwamnoni, lallai in har za a yi wa talakawa irin wannan gatan za a taimaka masu su san mutanen kirki masu son kawo ci gaban su da masu hana musu ci gaba.
Domin talaka mai zabe tamkar makaho ne, ba ya rarrabewa da barcin makaho, ana dai yi masa kwarjini da dadin baki, kwalliya, mota mai tsada, gida na gani na fada, a kuma a watsa masa ’yar tsaba, ya yi gaba, ba tare da sanin irin illar da ake yi masa ba. Kuma hakan zai magance matsalar na ta ka ci, ba ka ci ba, ka ci.
Kuma a sa sanda a kori siyasar ubangida da ta kudi a qasar nan. Wannan ma zai taimaka a daina cushe ko kitso da qwarqwata.
Kuma wani abin mamaki sai ka yi tambaya ina sarakunan gargajiya da malaman addini da masu hali da masu fada a ji da ’yan boko, me zai sa ba za su tsaya kai da fata su tace duk wasu ’yan takara tun daga matakan qananan hukumomi a har zuwa matakin tarayya, a tabbatar da cancantar kowane dan takara. Idan aka yi haka, to za a haifar da da mai ido wajen zabo nagartattun da za su yi wa al’umma jagora.
Abdullahi Idris Yakasai
Adi®eshin Email: [email protected] Lambar waya: 08054407095