✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsaloli 5 da suka addabi ’yan Najeriya

A yanzu Buhari yana shekararsa ta ban-kwana da gadon mulkin Najeriya da zai kammala wa’adinsa na biyu.

A yayin da ya rage wata goma wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshe, za a iya cewa wannan ce shekararsa ta ban-kwana da gadon mulkin Najeriya da zai kammala wa’adinsa na biyu.

Sai dai a yayin da yake shirin kammala wa’adin nasa, al’ummar kasa na cikin jimamin matsalolin rayuwa daga suka hada da matsalar man fetur da wutar lantarki da ilimi da abinci da kuma uwa-uba, matsalar tsaro.

Alkawuran Shugaba Buhari:

A farkon shekarar 2015, lokacin da Shugaba Buhari ke yawon yakin neman zabe a karkashin Jam’iyyar APC, ya bayyana cewa zai mai da hankali a kan al’amura uku idan ya samu nasarar zama Shugaban Kasa, wadannan kuwa su ne, yaki da almundahana da cin hanci da yaki da ’yan ta’adda, musamman ’yan Boko Haram da ke kashe mutane da lalata dukiyoyinsu a Arewa maso Gabas da kuma cewa zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

A wancan lokaci, a karkashin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, babu shakka al’amura sun tabarbare, al’umma na kuka da matsalolin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasa da rashin aikin yi da kuma makamantansu.

A daidai lokacin, kananan hukumomi sama da biyar suna karkashin ikon ’yan ta’addan Boko Haram a Jihar Borno.

Haka a jihohin Yobe da Adamawa da makwabtansu, al’umma na fuskantar kashe-kashe.

’Yan Boko Haram sun kwashe daliban makarantar sakandaren Chibok sun kai su daji.

A Abuja, ’yan ta’addar sun kai hare-haren bam a hedikwatar ’yan sanda da ofishin Jaridar This Day da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda suka tayar da bam a wani coci da ke Madalla.

A takaice dai al’amuran tsaro sun gama sukurkucewa, al’umma na cikin firgici da tsoro.

A yayin jawabinsa a dandamalin yakin neman zabe a Fatakwal, Jihar Ribas a Janairun 2015, Buhari ya bayyana cewa: “Babbar matsalar da ke damun kasar nan ita ce rashin tsaro da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasa, wadanda cin hanci da rashawa suka kaurara.

“Ina tabbatar maku da cewa za mu tattara jajirtattun ’yan Najeriya da za su gyara wadannan matsaloli.

“Ina kira gare ku, ku gane cewa, barnar da aka yi wa kasar nan babba ce. Rashin aikin yi ya ta’azzara, rashin tsaro ya girmama kuma ba za mu taba yarda da haka ba.

“Aniyarmu ta kawo gyara ta fara, za ta dauki lokaci, za ta bukaci hakuri, za ta bukaci tallafi da goyon baya daga gare ku, domin ganin mun yi nasara,” inji Buhari.

Al’amuran tsaro:

A matsayinsa na tsohon soja, al’ummar Najeriya sun sa tsammani mai girma a kan Shugaba Buhari, cewa lallai zai magance matsalolin tsaro da suke addabar Najeriya.

Shi da kansa ma ya yi alkawarin daukar kwararan matakai cikin sauri don magance matsalar ’yan Boko Haram a jihohin Arewa maso Gabas, sannan ya ba da tabbacin kawo hadin kai a kasa gaba daya.

Kasancewar a yau saura kasa da shekara daya Shugaba Buhari ya kammala mulkinsa, shin yaya al’amuran tsaro suka kasance a Najeriya?

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa daga 2015 zuwa bana, gwamnati ta kashe kimanin Naira tiriliyan hudu a harkar samar da tsaro.

A halin da ake ciki, za a iya cewa an samu sauki a jihohin Arewa maso Gabas, duk da cewa har yanzu akwai mutane da dama a sansanonin gudun hijira a Jihar Borno kuma daga lokaci zuwa lokaci ’yan ta’addar Boko Haram kan kai hare-hare a yankunan.

A jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya, an samu farfadowar Kungiyar Neman Kafa Kasar Biyafara (IPOB), wacce ta haddasa kashe-kashe da lalata dukiyoyin al’umma.

Rahotanni sun nuna yadda ’ya’yan kungiyar suke kashe jami’an tsaro da kona ofisoshin ’yan sanda, kamar yadda suka rika hallaka ’yan Arewa mazauna yankunnansu da cinna wa dukiyoyinsu wuta.

Wannan ta kai ga jami’an tsaro suka kama madugun kungiyar Nnamdi Kanu, wanda har zuwa yanzu yana fuskantar shari’a.

A jihohin Kudu maso Yamma kuwa, Kungiyar Samar da Kasar Oduduwa ta haddasa tashe-tashen hankali, a karkashin shugabancin Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, wanda shi ma yana fuskantar shari’a.

Kungiyar ta haddasa kashe-kashen mutane da lalata dukiyoyi a yankunan nasu. A Arewa maso Yamma kuwa, tabarbarewar tsaro ta kai intaha, inda musamman a jihohin Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Katsina da Kaduna ’yan bindiga ke yankan kauna son ransu.

Haka ma a jihohin Neja da Filato, Taraba da Nasarawa da Babban Birnin Tarayya, Abuja, a kullum ana samun rahotannin yadda ’yan ta’addar ke garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

A jihohin Zamfara da Sakkwato da Kebbi, ’yan ta’addar sun addabi al’ummomin karkara, sun hana noma da kiwo. Barayin sun ta da kauyuka da dama, a yayin da suka kashe mutane masudimbin yawa.

A yanzu haka, suna rike da mutane sama da 40, wadanda suka kama a harin da suka kai wa jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kuma suna rike da daliban Makarantar Bethal Baptist, Kujama, Kaduna. Kuma bayanai sun ce a cikin shekara biyu, sun kama limaman coci 62, sun nemi kudin fansa kimanin Naira miliyan 540.

’Yan ta’adda sun kashe manyan jami’an tsaro, na baya-bayan nan, shi ne Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda mai kula da shiyyar Dutsin-ma.

Sun kai wa motocin ayarin Shugaban Kasa hari a hanyarsu ta zuwa Katsina a yankin Dutsin-ma. A kwanakin baya kuma sun fasa gidan yarin Kuje, Abuja, inda suka tserar da manyan masu laifi fiye da 600.

A yanzu ma sun sha alwashin cewa za su yi garkuwa da shi kansa Shugaban Kasa da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i.

Ta la’akari da matsalar tsaro da ke addabar Najeriya, ko za a iya cewa Shugaba Buhari ya cika alkawarinsa dangane da tsaro?

Tambayar da aka yi wa mai fashin baki kan al’amuran yan da kullum, Dokta Abubakar Kari ke nan, inda ya amsa da cewa Gwamnatin Buhari ta gaza ta muhimman fuskoki uku, wadanda suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasa da yaki da almundahana da kuma tabbatar da tsaro.

A fuskar tsaro, hatta masoya Buhari na gaske sun san cewa Najeriya na fuskantar matsalar tsaro fiye da yadda take a 2015.

’Yan ta’adda, masu garkuwa da mutane don amsar kudin fansa da masu fakewa da kabilanci da masu daukar bindiga da ake cewa ba a san su ba, suna ta kashe mutane, suna sacewa da lalata dukiyar mutane.

Kuma babu shakka wannan babban abin firgici ne kuma abin mamaki ne da hakan ke faruwa a karkashin mulkin Buhari.

Shi kuwa Shugaban Al’ummar Ijaw, Cif Edwin Clark, cewa ya yi “Ni dai a ra’ayina, ba mu da gwamnati a kasar nan. A matsayinmu na ’yan Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ba ya aikin komai…”

Wutar lantarki:

Samar da ingantacciyar wutar lantarki na daga cikin alkawuran da Shugaba Buhari ya yi wa al’ummar Najeriya.

A yayin da yake jawabin amsar ragamar mulki a 2015, ya ce babu wani dalili da za a ce Najeriya ta rasa wutar lantarki, don haka ya dauki alkawarin kawo canji a wannan fuska.

Shugaba Buhari ya ce, “Babu wani dalili ko daya da za a iya gaya wa al’ummar Najeriya da ya haddasa tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan da ya haddasa rashin wutar lantarki.

“Abin kunya ne ga kasa mai al’umma sama da miliyan 180 amma tana samar da wutar lantarki Megawat 4,000 kacal kuma tana raba kasa da haka.

“Gwamnatocin baya sun salwantar da kimanin Dala biliyan 20 daga 1999 amma ba su iya samar da komai ba sai duhu, takaici da talauci ga al’ummar Najeriya.

“Ba za mu lamunci haka ta ci gaba da faruwa ba. Za mu yi nazari na tsanaki domin samo hanya mafi sauri da sauki ta samar wa ’yan Najeriya wutar lantarki,” inji Buhari.

Sai dai kuma ga dukkan alamu wannan alkawari bai cika ba, domin kuwa har zuwa hada rahoton nan, babu ingantacciyar wutar lantarki a Najeriya.

Hukumar Kula da Al’amuran Lantarki (NESO) ta bayyana a cikin watan Mayu da ya gabata cewa Najeriya na samar da Megawat 3,522.80, kasa da Megawat 4,000 da Gwamnatin Buhari ta gada a 2015.

Kuma a cikin shekara biyu da ta gabata, an samu durkushewar lantarki a dukkan Najeriya sau shida.

A sakamakon rashin ingantacciyar wutar lantarki, a Kano kadai, an samu rufe manya da matsakaita da kananan masana’antu da yawa.

A rukunin masana’antu na Sharada da Dakata, layuka da dama na kamfanoni baki daya sun daina aiki, a wasu layukan kuma akwai ’yan kalilan da ba su fi uku ba da wakilanmu suka samu suna aiki.

Wadanda suka riska suna aikin, da dama sun rage yawan aikin da suke yi, ko sun rage kwanakin aikin, ko sun rage ma’aikata.

Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu ta Jihar Kano, Hussaini Saleh da ke Unguwar Masana’antu ta Sharada ya ce samun tsayayyiyarwutar lantarki shi ne kashin bayan kowace sana’a da ke son dorewa, don haka rashin wutar lantarkin da ita ce mafi araha a Najeriya ya durkusar da fiye da kashi 60 cikin 100 na masana’antun da ke jihar.

Ya ce a baya iskar gas ke biye wa wutar lantarkin wajen araha amma yanzu ita ma ta yi tsadar da kamfanoni sun gwammace su sayi fetur duk tsadarsa su yi ayyukansu da shi.

“Dubi farashin man dizal yadda ya yi ninki uku na kudin wutar lantarki, daga lita daya kan Naira 200 zuwa Naira 700, gaya min yadda masu karamar sana’a za su samu riba idan suka yi aiki da shi?

“Mun samu labarin yadda wasu daga cikin kamfanonin suka dawo yin rabin aikin da suke yi a da, wasu kuma kashi 25 kawai za su iya yi, wasu sun durkushe ke nan har abada, duk saboda tsadar wadannan sinadaran,” inji shugaban.

Fannonin ilimi/fetur da noma:

A fannin ilimi, labarin dai irin na jiya ne, domin kuwa makarantun gwamnati na fsukantar matsaloli daban-daban, wadanda suka hada da yajin aikin malamai da rashin ingantattun azuzuwa da kayan aiki.

Zuwa hada rahoton nan, dukkan jami’o’in Najeriya suna kulle tsawon wata biyar babu karatu, domin Kungiyar Malaman Jami’a tana yajin aiki kan matsalolin da suka shafi ko in kula daga gwamnati.

Kuma mafi yawan makarantun da ke yankunan da ’yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka, kamar jihohin Zamfara da Kebbi da Sakkwato da Katsina da sauransu, suna kulle, babu karatu saboda tsoron ’yan ta’adda da kan fasa makarantu su kwashi dalibai.

Matsalar man fetur kuwa ta zama ruwan dare a Najeriya, domin daga zuwan Gwamnatin Buhari a 2015 zuwa yau, an kara farashin fetur sau uku. Duk da haka kuma ana samun karancinsa a gidajen mai.

Man jirgi da gas na girki da dizal da kananzir duk farashinsu ya yi tashin gwauron zabo.

Wannan na daga dalilan da suka sa farashin kayan masarufi da kudin sufuri suke hauhawa.

A fannin noma da kiwo, manoma da makiyaya, musamman a Arewa suna fuskantar matsalolin da suka hada da rashin takin zamani kuma ga shi ya yi tsada, ga matsalar ’yan bindiga da suka hana manoma da dama yin noma a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Sakkwato da Neja da wasu sassan Borno da sauransu.

Masu sharhin kan al’amuran yau da kullum sun ce abu ne mai matukar wuya, Shugaba Buhari ya iya cika alkawuransa, idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa a wadannan sassa biyar.

Sun ce abin da ya hana kasa aiwatarwa tsawon shekara bakwai, ba zai iya aikata shi nan da wata goma ba. Ko yaya gaskiyar wannan hasashe? Lokaci ne dai kadai zai nuna.