✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Za mu gana da Buhari — NGF

Gwamnoni 36 na jihohin Najeriya sun yanke shawarar ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin gaggawa domin tattauna wa kan dabarun magance matsalar tabarbarewar tsaro…

Gwamnoni 36 na jihohin Najeriya sun yanke shawarar ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin gaggawa domin tattauna wa kan dabarun magance matsalar tabarbarewar tsaro da ta addabi kasar.

Cikin wata sanarwar da Kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF ta fitar a ranar Juma’a, ta ce za ta za ta goyin bayan duk wani kudiri na yi wa Rundunar ’Yan sandan kasar garambawul domin inganta tsaro a fadin kasar.

Shawarar da Kungiyar Gwamnonin ta yanke yayin zamanta na 22 da ta gudanar a ranar Larabar da ta gabata, na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa wasu manoman shinkafa a Garin Kwashebe na Karamar Hukumar Jere a jihar Borno.

Gwamnonin sun kuma tattauna kan yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), inda suka bukaci Gwamnatin Tarayya da kungiyar su hanzarta warware sabanin da ke tsakaninsu don ba da damar sake bude manyan makarantun kasar nan.

Aminiya ta ruwaito cewa Gwamantin Tarayya ta ce kiraye-kirayen neman Shugaba Buhari ya yi murabus daga matsayinsa saboda tabarbarewa tsaro alama ce ta rashin sanin ya-kamata.

Ministan Yada Labarai, Kai Mohammed ya bayyana haka a lokacin ganawarsa da Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya (NPAN).

Ministan ya ce neman Shugaba Buhari ya yi murabus saboda lalacewar sha’anin tsaro “shigar kazamar siyasa ce cikin al’amarin tsaro”.