Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce matsalolin tsaro sun ja baya a fadin Najeriya tun da Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya.
Ribadu ya kuma ce Tinubu bai cika yawan surutu ko cika baki ba a kan nasarorin da ya samu a bangaren na tsaro tun bayan darewarsa karagar mulki.
- Kotu ta soke zaben Gwamnan Zamfara, ta bayyana shi a matsayin ‘inconclusive’
- An ‘harbi’ masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Kaduna
Ya bayyana haka ne a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, yayin taron shekara-shekara na Editoci na Najeriya ranar Alhamis.
Sai dai ya ce gwamnati mai ci ta karbi mulki ne a daidai lokacin kasar nan ke cikin tsaka mai wuya.
Ya kuma ce matsalar tsagerun Neja Delta da ta masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara yanzu sun yi haya matuka.
Ya ce amma duk da waɗannan nasarorin, dole sai an haɗa karfi da ƙarfe wajen daƙile ragowar ƙalubalen tsaro.
Ribadu ya kuma ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro rayuka da dukiyoyinsu.