✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke zaben Gwamnan Zamfara, ta bayyana shi a matsayin ‘inconclusive’

Kotun ta ce za a sake zabe a wasu ƙananan hukumomi 3

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta a ranar Alhamis ta soke nasarar Da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya samu.

A sakamakon haka, kotun ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Kotun dai ta ce za a sake zaben ne a wasu Kananan Hukumomin Jihar guda uku.

Kananan Hukumomin su ne Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukyun.

A cewar kotun, hukuncin da Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan ya yi a baya, wanda ya tabbatar da nasarar Dauda, bai yi la’akari da hujjar da jam’iyyar APC mai kara ta gabatar ba.

Kazalika, kotun ta yi fatali da sakamakon da APC da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayar a Karamar Hukumar Maradun.

Tsohon Gwamnan Jihar, kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle ne dai ya shigar da karar yana neman a soke nasarar Dauda a zaben.

Hukumar INEC dai ta bayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.