✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano

Kotun Ɗaukaka Kara ta Tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanar cewa gobe za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Kano tsakanin Gawuna da…

Kotun Ɗaukaka Kara ta Tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya gobe Juma’a, 17 ga watan Nuwamba a matsayin raanr da za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Kano da ke gabanta.

Kotun ta bayyana cewa zaman nata zai kasance ne da misalin karfe 10 na safe, inda za ta sanar da hukuncinta kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daukaka zuwa gabanta kan soke zaɓensa da Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaben Gwamnan Kano ta yi.

“Wannan bayani na kunshe cikin sakon da kotun ta turawa lauyoyin mu a yau,” a cewar kakakin Gwamnan Kano, Sanusi Bature.

Gwamna Abba na Jam’iyyar NNPP ya daukaka kara ne bayan a watan Satumba kotun sauraron karar zaben gwamnan Kano ta soke nasararsa a zaben watan Maris, ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara.

NNPP da Abba, wanda shi ne kadai gwamnanta, sun bayyana hukuncin kotun farkon a matsayin rashin adalci, suka kuma daukaka kara da fatan za ta dawo masa da kujerarsa.

A ranar 20 ga watan Satumba, 2023, alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin mai shari Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay suka soke nasarar Abba, bayan sun soke 165,663 daga cikin kuri’un da ya samu a matsayin ba halastattu ba.

Alkalan sun soke kuri’un ne bisa hujjar rashin kwanan wata da kuma rashin hatimin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a jikin takardun kuri’un, abin da Gwamna Abba ya kira “rashin adalci” da kuma yi wa “tsarin shari’a dibar karan mahaukaciya.”

A kan haka ne ya yi alkawarin daukaka kara tare da bayyana kwarin gwiwar zai samu adalci a kotun gaba.

A ranar 18 ga watan Maris INEC ta ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da kuri’u 1,019,602 a yayin da Gawuna ya zo na biyu da kuri’u 890,705.

Amma bayan soke 165,663 daga kuri’un da Abba ya samu, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta bayyana bayyana cewa kuri’unsa sun koma 853, 939, a yayin da Gawuna mai kuri’u 890,705 ya sha gabansa.