✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaro: Shugaban Ƙaramar Hukuma ya tabbatar da haɗa kai da Sarakuna

Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu shida da ke ƙaramar hukumar,

Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar.

Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu shida da ke ƙaramar hukumar, inda ya jagoranci ɗaukacin jami’an majalisar ƙaramar hukumar don gudanar da ziyarar.

A dai cikin makon nan ne Shugaban ƙaramar hukumar tare da tawagarsa suka ziyarci fadar Sarkin Kagoma, Mista Paul Zakkah Wyom; Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu; da Tum Nikyob, Mallam Tanko Tete. Ya bayyana godiyarsa tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da aikinta cikin gaskiya da amana.

Ya jero wasu daga cikin nasarorin da majalisarsa ta cimma, ciki har da biyan kuɗin WAEC da JAMB ga ɗalibai 550 da kuma samar da guraben aiki ga wasu ‘yan yankin. Ya kuma jaddada ayyukan ci gaba da Gwamna Uba Sani ke aiwatarwa, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin gwiwa.

A yayin da suke mayar da martani, sarakunan gargajiyan sun yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa ziyarar da ya kawo, tare da gabatar masa da matsalolin da suka addabi yankunansu, ciki har da lalacewar hanyoyi, rashin ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya, ƙarancin ruwan sha da kuma matsalolin tsaro.

Ziyarar ta ci gaba a ranar Laraba zuwa masarautun Zikpak, Godogodo, da kuma Barde, inda a  kowanne fada, Mista Dogara ya sake jaddada ƙudirinsa na kyautata rayuwar al’umma da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin majalisar ƙaramar hukumar da sarakunan gargajiya.

Agwam Zikpak, Mista Josiah Kantyok, ya nanata buƙatar zaman lafiya a matsayin tushen ci gaba. Hakazalika, Sarkin Godogodo, Reɓerend Dakta Habila Sa’idu, ya roƙi majalisar da ta magance matsalolin kan iyaka tsakaninta da maƙwabtanta, yayin da Sarkin Barde, Mista Njebi Daniel Lemson, ya bayyana damuwarsa kan matsalar tsaro da ke addabar yankinsa.