Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus sanadiyar kalaman da ya yi a kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.
Secondus ya yi wannan martani ne a ranar Asabar ta hannun mai ba shi shawara a kan kafafen watsa labarai, Mista Ike Abonyi.
- Buhari ya nemi gafarar iyayen daliban da aka sace —PDP
- Na fi cancanta in zama shugaban PDP- Secondus
- Jonathan na da ’yancin tsayawa takara a zaben 2023 —PDP
- Garba Shehu ya ba ’yan Najeriya hakuri kan cewa dalibai 10 aka sace
Furucin da Shugaban Kasar ya yi a ranar Alhamis na cewa katabus din da jami’an tsaro ke yi bai wadata ba wajen magance ayyukan ta’addaci a kasar nan shi ne ya fusata Shugaban na PDP.
“Na yi mamakin kalaman Buhari, duk da irin kiraye-kirayen da aka rika masa a kan ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar nan, amma ya yi kunnen uwar shegu da mutane, sai kuma a yanzu zai ce sun gaza.
“A matsayinsa na Shugaban kasa, kuma Kwamandan tsaro, ya kamata ya daina kame-kame ya amsa cewa ya gaza,” in ji Secondus.
Ya kara da cewa kalaman na Buhari ba komai ba ne, face gazawa da kasa shawo kan matsalar tsaro, dan haka babu sauran wani uzuri da za a masa face ya yi murabus.