Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta sun haddasa barazanar karancin abinci a kasar nan.
Magashi wanda ya bayyana hakan a matsayin wata sabuwar barazana da ta kunno kai a kasar, ya yi wannan bayani a ranar Litinin yayin bude taron sanin makamar aikin da Hukumar Leken Asiri ta Sojoji (DIA) ta gudanar a Abuja, babban birnin kasar.
- Wasu matasa sun guntule wa juna hannu a Yobe
- Babu wani soja da ke da hannu a harin da aka kai mana — NDA
An shirya taron ne ga Mashawartan Fannin Tsaro da kuma wakilan Hukumar Tsaro da ke aiki a Ofisoshin Jakadun Najeriya a ketare.
Magashi ya ce hare-haren da mayakan Boko Haram da na ISWAP ke ci gaba da kaiwa a yankin Arewa maso Gabas da kuma hare-haren da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da barayin shanu da kuma rikicin makiyaya da manoma a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sun zama babbar barazana ga tsaron Najeriya.
Magashi ya ce su kuma wasu daidaikun jihohin Kudu maso Kudu na fama da barayi masu fasa bututun mai, ’yan ta da zaune tsaye, masu fasa kwauri ta ruwa, yayin da yankin Kudu maso Gabas kuma ke fama da ’yan kungiyar IPOB masu fafutikar ballewa daga Najeriya.
Kazalika, ya ce yankin Kudu maso Yamma na fama da masu ra’ayin kafa kasar Yarabawa masu kabila daya, kuma a can ma ana fama da tashe-tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma.
“Babban abin takaicin, wannan matsalar rashin tsaro ba ga tsaro kadai take kalubale ba, har ma ga abinci ta zama babbar barazana.
“Musamman a halin yanzu ana fuskantar karancin abinci da kuma yawaitar hauhawar farashin kayan abincin a fadin sassan kasar nan.
“Saboda haka abu ne mai muhimmanci dukkan bangarorin tsaron kasar nan su hada hannu wuri daya domin samar da tsaron da zai kakkabe wadannan barazana da kasar nan ke fuskanta.”
Aiwatar da hakan a cewar Magashi zai sake zaburar da jama’a wajen bunkasa tattalin arziki da kuma samar da yanayin da masu zuba jari daga waje za su bijiro ga Najeriya.
Ya ce jami’an tsaro sun taka rawar gani matuka, inda nasarorin da suke samu ne ta kai ga har aka samu ’yan ta’adda sama da 14,000 suka sadudu tare da ajiye makamai.