Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bukaci a sauya tsarin shugabancin kasar (restructuring), domin magance matsalar tsaro da ke addabar ta.
Obasanjo ya ce yin hakan shi ne mafita saboda gwamnatoci a dukkan matakai na kara nuna gazawarsu su majance matsalar tsaro a yankunan da ke karkashinsu.
A cewarsa, mafita daga matsalar ita ce a mike yanzu a hada kai mai tattare da kishin kasa da jajircewa da kuma hangen nesa, da zummar magance matsalar tsaro.
“Lokaci ya wuce na kiraye-kiraye ga gwamnatoci da suka gaza. Mu kirkiro mu kuma jagornaci matakan da za su hada gwamnatoci da jama’a wurin tsarawa da aiwatar da matakan tsaro da kuma daukar alhakinsu”, inji shi.
- ‘Yan bindiga: Gwamnatinmu ta gaza —Gwamnan Katsina
- Lawan ya gaya wa Buhari yadda zai kori hafsoshin tsaro
- Manyan hafsoshin tsaro sun gaza, ba su da uzuri —Buhari
Obasanjo ya ce yin shiru ko neman ballewa daga kasar saboda matsalolin tsaro ba su ne mafita. Amma matukar ba a koma tsarin shugabanci na yankuna ba, to haka kasar za ta yi ta tafiya ba tare da an kawo karshen matsalar tsaro ba.
Ya bayyana haka ne a wata ganawa da aka yi da shi a ranar Juma’a a Abeokuta, Jihar Ogun a lokacin taron tunawa da Sobo Sowemimo na 2020.
Matsalar tsaro ta addabi Arewacin Najeriya
Kalaman tsohon shugaban na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan an yi ta zanga-zanga a wasu sassan Najeriya, musamman jihar Katsina, mahaifar Shugaba mai ci Muhammadu Buhari inda ‘yan bindiga ke karkashe jama’a suna kuma garkuwa da wasu.
Gwamna jihar, Aminu Masari ya amsa cewa gwamnatinsa ta gaza wajen kare jama’a, yayin da Shugaban Kasar ya ce Manyan Hafsoshin Tsaro sun nuna gazawa aa aikinsu kuma ba su da uzuri.
Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane; Arewa ta Gabas kuma na ci gaba da fama da matsalar ‘yan Boko Haram, musamman jihar Borno. Jihohin Arewa ta Tsakiya kuma sun fi fama da rikicikin kabilanci da na manoma da makiyaya baya ga wasu nau’ukka na rashin tsaro.