✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro na barazana ga kasancewar Najeriya kasa daya – Gwamnonin Arewa

Kungiyar ta ce ya zama wajibi a magance matsalar wadda a yanzu ke barazana ga ci gaba da kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa.

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NGF) ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa tawagar Gwamnan jihar Bunuwai, Samuel Ortom ranar Asabar inda ta bukaci a yi zuzzurfan bincike a kai.

Kungiyar ta ce ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen lalubo bakin zaren matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya, wadda a yanzu ta ce na barazana ga ci gaba da kasancewarta dunkulalliyar kasa.

Shugaban Kungiyar, kuma Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa, Makut Macham ya ce harin wani yunkurin bata-gari ne na tayar da zaune tsaye a jihar ta Binuwai da ma kasa baki daya.

A ranar Asabar ne dai aka kai wa tawagar Gwamna Ortom harin a kauyen Tyomu dake kan hanyar Makurdi zuwa Gboko, duk da dai ya sami kubuta ba tare da ko kwarzane ba.

Daga nan sai Gwamna Lalong ya yabawa jami’an tsaron dake gadin lafiyar Ortom din kan yadda suka yi kokari wajen kubutar da shi daga maharan da ma sauran ’yan tawagarsa.

Shugaban Kungiyar ya kuma ce Gwamnonin Arewa na tare da Ortom da ma dukkan al’ummar jihar Binuwai.

Ya kuma ce za su ci gaba da hada gwiwa da sauran jami’an tsaro a kokarinsu na kawo tsaro da zaman lafiya a Arewa da ma Najeriya baki daya.