Mabiya Darikar Kadiriyya a Najeriya sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman dauki daga Allah Ya kawo karshen mastalar tsaro da ta addabi kasar, musamman a yankin Arewa.
Da yake jagorantar taron addu’o’in, Shugaban Darikar Kadiriyya na Afirka ta Yama, Sheikh Muhammad Karibullah Nasiru Kabara, ya ce gudanar da irin addu’o’in a duk lokacin da wani bala’i ya samu mutane, koyarwa ce ta Annabi Muhammad (SAW).
- Turji: Kasurgumin dan bindigar da ya addabi Zamfara Na neman a yi sulhu
- ‘China ba za ta kwace kadarorin Najeriya ba saboda taurin bashi’
“Idan muka yawaita addu’o’i, Allah zai amsa rokonmu kuma in Allah Ya yarda Allah zai fitar da mu daga wannan hali da muke ciki,” saboda haka yin shi abu ne mai muhimmanci idan aka shiga cikin tsanani, inji malamain.
Shugaban na Kadiriyya ya kuma bayyana cewa gudanar da addu’ar ta zama dole duba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya da sauran sassan duniya, wanda abin damuwa ne.
Sheikh Karibullah ya yi kira ga daukacin ’yan Najeriya da su dage da rokon Allah Ya kawo karshen matsalar tsaro, sannan su tuba ga Allah su daina aikata sabo.
Ya yi kira da a ci gaba da yin addu’o’in a kullum tare kulla kyakkyawar mu’amala da nuna kyawawan dabi’u a tsakanin mutane da kuma tsakaninsu da Mahaliccinsu.
“Mu koma mu duba yadda tsakaninmu yake da Mahaliccinmu, mu tuba, mu daina aikata sabo, mu rika taimakon marasa shi tare da yin biyayya ga mahaifa,” inji malamin.
Shugaban na Kadiriyya ya kara da cewa ana bukatar mata da kananan yara da tsofaffi su rika halartar irin wadannan taruka, saboda haka ya bukaci a isar da sakon ga wadanda ba su samu halartar na ranar Lahadin ba.