Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewar jami’an tsaro sun gayyaci Malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi domin amsa tambayoyi game da kalamansa a kan ’yan bindiga.
Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Litinin.
- Mazauna karkara na neman daukin ruwan sha a Gombe
- Jami’in Binance ya tsere daga hannun mahukuntan Nijeriya
Gumi dai ya dage kan akwai bukatar yi wa ‘yan bindiga afuwa tare da tattaunawa da su domin tabbatuwar lafiya.
Da yake amsa tambayoyi a Aso Rock, Idris ya ce: “Gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa wajen samun bayanan da za su magance matsalarmu.
“Jami’an tsaro sun tashi tsaye. Gumi da duk wani a kan wannan lamari ba su wuce doka ba.
“Idan yana da shawarwarin da ya kamata ya bai wa jami’an tsaro ko kuma wani abu da ake bukatar magancewa, za su yi abin da ya dace.
“Babu wanda ya fi karfin doka kuma ina sane da cewa shi ma hukumomin tsaro sun gayyace shi domin amsa tambayoyi.
“Idan ka yi kalaman da suka shafi tsaron kasa, ya zama wajibi ga hukumomin tsaro su yi bincike kuma suna yin binciken, don babu wanda ya fi karfin doka.”
Idan ba a manta Sheikh Gumi ya sha yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tattauna da ’yan bindiga dangane da laifukan da suka aikatawa na garkuwa da mutane domin magance matsalar.