✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Kudu sun nemi Buhari ya kira taron gaggawa

Yakasai ya ce babu wani taro da zai magance matsalolin Najeriya a wannan lokaci.

Gwamnonin Jihohi 17 na Kudancin Najeriya sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kira wani taron gaggawa domin tattauna kalubalen tsaro da yankinsu ke fuskanta.

Kungiyar gwamnonin Kudancin ta yi wannan kira ne yayin taron da ta gudanar ranar Talata a Asaba, babban birnin Jihar Delta.

Wata sanarwa da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya fitar ta ce taron zai kasance yadda za a hada kai domin magance matsalolin tsaro da yankin Kudancin Najeriya ke fuskanta.

Haka kuma, Gwamnonin sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya fito ya yi wa ’yan Najeriya jawabi dangane da matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar baki daya.

Sai dai daya daga cikin Dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya ce babu wani taro da zai magance matsalolin Najeriya a wannan lokaci, inda ya shawarci gwamnatin tarayya da ta sake yin bita kan tarukan da aka yi a baya, ta zabi batutuwan da za su hadan kan kasar sannan a aiwatar da su.