Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce mafita daya daga matsalar tsaro da kasar nan ta samu kanta a ciki ita ce kowa ya koma ga Allah ya nemi gafararsa.
Sanatan mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya yi wannan kalamai ne a tattaunawarsa da Aminiya a Abuja, inda ya ce idan jama’a suka koma ga bin tafarkin da Allah Ya shimfida wannan bala’i da ake ciki zai kau.
- Wankan kududdufi ya yi ajalin dan shekara 14 a Kano
- Irin matan da bai kamata a yi masu kishiya ba – Dr. Ahmad Gumi
“Ya zama dole mu tabbatar da muna bincikar kawunanmu da yadda muke tafiyar da rayuwarmu, shin muna adalci ga junanmu, muna bin koyarwar da Mahaliccinmu ya dora mana, tun daga kan maigida da iyalansa, zuwa kan mu masu rike da madafun iko, muddin ba haka muke ba, to yana da wahala mu fita daga halin da muka tsinci kanmu a ciki,” inji shi.
Sanata Shekarau wanda shi ne Sardaunan Kano ya kuma ce an samu ci gaba bayan komawa ga tsarin dimokuradiyya, inda ya ce ko Amurka da Najeriya take koyi da ita, wadda ta shafe fiye da shekara 200, tana bin tsarin dimokuradiyya tana yin kuskure, balle Najeriya da a yanzu ne ta yi shekara 22, tana bin tsarin.
Ya ce, “A nawa ganin har yanzu koyo muke, kuma an samu nasara sosai, domin ko tarihin da dimokuradiyya ta kawo abin yabawa ne.
“Ko yadda Jam’iyyar APC ta karbi mulki daga hannun Jam’iyyar PDP, na nuni da cewa dimokuradiyyar ta kankama, sai dai mu kara hakuri, a kan wasu abubuwa domin babu abin da yake tabbatacce.”
Malam Ibrahim Shekarau ya kuma bukaci su jami’an tsaro su kara himma, don tabbatar da zaman lafiya a kowane sashi na kasar nan.
Ya ce, babu wata takaddama da take addabar jam’iyarsu ta APC, inda ya ce dole ne idan gida ya girma a samu ’yan rigingimun da ba a rasa ba, amma hakan ba ya nufin jam’iyar tana fama da rikici.
Game da halin da jam’iyar take ciki a Jihar Kano, Sanata Shekarau ya ce yana da yakinin rigimar da take fuskanta ba wata babba ba ce da za ta daga hankali, lura da yadda a ’yan kwanakin nan jam’iyar ta yi babban kamu na jiga-jigan ’yan siyasa, inda ya ce hakan manuniya cewa farin jinin APC a jihar yana nan, don haka yana da kyakkyawan zaton samun nasara ga jam’iyyar a zaben 2023 a jihar da kasa baki daya.
Sanata Shekarau ya bukaci a yi adalci wajen ba kowane dan jam’iyyar da ya cancanta damar tsayawa takarar duk wani mukami, tun daga kan shugaban jam’iyya a mazabu zuwa kananan hukumomi da jihohi.
Ya ce, “Na san Gwamna yana da karfi a zaben shugabanni, amma yin adalci ne mafita ga ci gaban jam’iyyarmu.”
Malam Ibrahim Shekarau ya shawarci Jam’iyyar APC kan ta mika tikitin takarar Shugaban Kasa ga Kudu idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu.
Ya ce yin hakan ne zai tabbatar da adalci a siyasar kasar nan, inda ya ce yana goyon bayan tsarin karba-karba.
Sanata Shekarau ya ce: “A cikin kundin tsarin mulkin Jam’iyyar APC ba a rubuta batun karba-karba ba, amma na amince akwai tsarin mulki na hankali.
“Misali yanzu tsarin shiyya-shiyya da ake gudanarwa ai ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, amma tsari ne mai inganci, yanzu babu abin da za ka yi ba ka shigo da wannan ciki ba.
“To haka ma lamarin shugabanci a tsakanin Kudu da Arewa, idan aka yi watsi da wannan to gaskiya ba a yi wa juna adalci ba.
“Ina ganin ya kamata mu yi hakuri mu jawo ’yan uwanmu na Kudu mu da muke daga Arewa saboda idan za a yi zabe, Arewa ita kadai ba za ta yi kuri’ar samar da Shugaban Kasa ba, haka Kudu ita kadai ba za ta yi ba, sai mun hadu kuma zaman tare muke yi.
“Abin da na yarda da shi shi ne ba ma wai shiyya-shiyya ba, babu wata jiha a kasar nan, da ba ta da wadanda za su iya shugabancin kasar nan,” inji shi.
“Dangane da batun ko Jam’iyyar PDP za ta yi galaba a kan APC idan ta fito da dan takarar daga Arewa, ina ganin adalci shi ne gaba, kuma nagartar wanda Jam’iyyar APC ta tsayar ne zai kai ga nasarar jam’iyyar a zaben 2023.