✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro: Buhari ya nuna damuwarsa

Buhari ya ce za a yi amfani da fasahar sadarwa wajen daga darajar kasar nan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar kasar nan, inda ya ce gwamnati ta nemo kwakkwaran mataki wajen magance lamarin.

Da ya ke magana ranar Juma’a a Abuja yayin bikin yaye daliban Kwalejin Tsaro ta Kasa (NDC), Buhari ya jadadda cewar gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen fitar da Najeriya daga cikin matsalar tsaro da take fuskanta.

– Fashewar Gurneti ta hallaka yara 5 a Borno
Da an biya min kudin fansa, da na ajiye aikina – Kwamishinan Neja

Buhari, wanda Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi mai ritaya ya wakilta, ya ce, “Ya kamata daliban da aka yaye ya su yi amfani da ilimin da kuma kwarewar da suka samu na wata 11 wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.”

Kazalika, ya ce gwamnatin Shugaba Buhari za ta dawo da martabar skasar nan ta hanyar kawo cigaba ta hanyar fasahar sadarwa.

A cewarsa, jajircewarsa ta amfani da cigaban fasaha ta bayyana karara a cikin manyan canje-canjen da aka samu a dimokuradiyyar kasa da yanayin siyasa.

Ya ce, “A bayyane yake wajen ci gaba da yakar cin hanci da rashawa, rarrabuwa ta fuskar tattalin arziki, sake fasalin bangaren mai da iskar gas, aiwatar da shirye-shiryen saka hannun jari domin kyautata rayuwa, aikin gona da sarrafa kayan amfanin gona ta amfani da abubuwan fasaha”.

A nasa bangaren, Kwamandan Kwalejin Tsaro ta Kasa, Rear Admiral Oladele Daji, wanda tun da farko ya ba da babbar lambar yabo ta NDC ga daliban da suka kammala karatun, ya bukaci Shugaban Kasa da ya gaggauta kammala ayyukan da aka fara a harbar dindindin na kwalejin da ke Piwoyi, Abuja.

Daji ya ce, kammalawa da kuma mayar da kwalejin zuwa matsuguninsa na dindindin zai kasance “babban abin farin ciki na bikin cika shekara 30 da kafa cibiyar.

%d bloggers like this: