✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Buhari ya gana da shugabannin INEC

Ana tsammanin zaman ya mayar da hankali kan hare-haren da aka kai wa INEC.

Shugaba Buhari ya gana da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) Mahmoud Yakubu da Kwamishinonin Hukumar.

Taron da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da sauransu.

Kazalika Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, Daraktan Hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi da Sufeton ’Yan Sanda, Usman Alkali Baba.

Daga cikin Kwamishinonin zabe da suka halarci ganawar akwai Misis May Agbamuche-Mbu da Barista Festus Okoye.

Sai dai ba a bayyana wa manema labarai dalilin yin taron ba.

Amma Aminiya ta gano taron na da nasaba da irin barazana da kuma kone ofisoshin INEC da wasu bata-gari ke yi, a yankin Kudu-maso-Gabas da kuma Kudu-maso-Kudu a baya-bayan nan.