✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Matsalar tsaro ba za ta shafi aikin kidayar jama’a na 2023 ba’

Hukumar ta ce za ta yi amfani da na'urorin zamani wajen kidayar

Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Nasir Isa Kwarra, ya ce duk da kalubalen tsaron da wasu sassan Najeriya ke fuskanta, hakan ba zai shafi aikin kidayar da za ta gudanar a 2023 ba.

Ya kuma ce za su yi amfani da na’urorin zamani yayin kidayar ta badi, kuma yanzu haka ma tana amfani da na’urorin shata taswirar zamani wajen kirga gidaje.

Nasir Kwarra ya bayyana hakan ne a fadar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, yayin wata ziyarar da ya jagoranci ma’aikatan hukumar suka kai masa ranar Litinin.

Shugaban ya kuma ce ya zuwa yanzu, hukumar ta shata Kananan Hukumomi 773 da ke kasar nan, in ban da guda daya da ta rage.

A cewarsa, “Wannan ziyarar tana daya daga cikin irin shirye-shiryen da muke yi gabanin kidayar jama’ar da za mu yi a 2023, don neman hadin kai da goyon bayan Sarakuna a matsayinsu na iyayen kasa.

“Shirye-shirye sun riga sun yi nisa, kuma muna ba da tabbacin cewa matsalar tsaro ba za ta shafi shirin ba.

“Muna amfani da fasahohin zamani wajen shata iyakoki da kidaya gidaje, kuma nan da watan Afrilun badi da za a gudanar da kidayar, kuma zai zama na zamani da izinin Allah,” inji shi.

Daga nan sai ya roki Sarkin da ya taimaka wajen yada sakon da kuma wayar da kan mutanen masarautarsa, ta bakunan Hakimai da Dagattai da Masu Ungawanni.

Da yake mayar da jawabi, Sarki na Kano, ya yi kira ga al’ummar jihar da su bayar da hadin kai ga ma’aikatan kidayar ta hanyar tabbatar da an kirga su.

“Kidayar jama’a na da matukar muhimmanci, saboda da ita ne gwamnati za ta san yawan al’umma domin ta tsara manufofi da kuma samar da ayyukan raya kasa. Ina ba ku tabbacin cewa za mu bayar da dukkan hadin kan da kuke bukata a dukkan masarautun jihar Kano guda biyar,” inji Sarkin.

Bayan ziyarar dai, Shugaban na NPC ya kuma jagoranci taron tattaunawa da sauran ma’aikatan hukumar, kuma ya sami rakiyar Kwamishinoni da manyan Daraktocin.