Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da tsawaita lokacin sake bude makarantu a Jihar saboda kalubalen tsaro.
A baya dai, Jihar ta sanar da ranar tara ga watan Agustan 2021 a matsayin ranar da za a sake bude makarantu don fara sabon zangon karatu na uku.
- Bidiyon Dala: Har yanzu Ganduje bai biya ni tarar da kotu ta umarta ba – Jaafar Jaafar
- Najeriya ba irin su Atiku ko Tinubu take bukata ba a 2023 – IBB
Sai dai gwamnatin ta ce ayyukan da dakarun soji ke gudanarwa yanzu haka ta sama da kasa kan ’yan bindiga a iyakarta da Jihohin Neja da Katsina da Filato da kuma Zamfara ba za su bari a sake bude makarantun ba.
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Shehu Usman Muhammad, da takwaransa na Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Samuel Aruwan, ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa ranar Juma’a.
Sun ce Jihar ta kuma umarci jami’an tsaro da su dada zafafa kai hare-hare a sabbin maboyar ’yan bindigar da aka gano a kwanan nan.
“Gwamnatin Jihar Kaduna ta karbi shawarwarin tsaron da aka bata, kuma a kan haka take umartar dukkan makarantu da su bi wannan umarnin sau da kafa.
“Za a sanar da sabuwar ranar sake bude makarantun da zarar al’amuran tsaro sun inganta,” inji sanarwar.