✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar tsaro: An kama jarogran zanga-zangar da aka yi a Katsina

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sanda sun kama Nastura Ashir Sharif, uban kungiyar Hadakar Kungiyoyin Arewa ta Northern Group Congress (CNG). Wasu mambobin kungiyar ta…

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sanda sun kama Nastura Ashir Sharif, uban kungiyar Hadakar Kungiyoyin Arewa ta Northern Group Congress (CNG).

Wasu mambobin kungiyar ta (CNG) sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan sandan sun tafi da Nastura Ashir Sharif Babban Birnin Tarayya inda suke tsare da shi zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Shaidun suka ce an kama shi ne jim kadan bayan da kungiyar ta shirya-zanga zangar lumana saboda yawan kashe-kashen jama’a da ‘yan bindiga ke yi a jihar Katsina.

Nastura Ashir Sharif, Shugaban Kungiyar CNG