✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: An haramta sayar da wasu samfuran Babura a Neja

’Yan bindiga sun koma karbar babura maimakon kudin fansar wadanda suka yi garkuwa da su.

Gwamnatin Jihar Neja ta haramta sayar da wasu samfuran babura masu kafa biyu a fadin jihar sakamakon matsalolin tsaro da yadda ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ke amfanin da baburan wajen kai hare-hare.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce matakin hakan ya biyo bayan matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar da kuma karuwar bukatar baburan da ’yan bindiga ke yi madadin karbar kudin fansar wadanda suka yi garkuwa da su.

Sanarwar da Matane ya fitar ta ce daga cikin baburan da aka haramta sayarwa akwai Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen da sauran babura wanda karfin injinsu ya kai 185cc zuwa sama.

Matane ya ce gwamnatin ta kirkiro wannan mataki ne a kokarin da take ci gaba da yi na hana ’yan bindiga sakat da sauran masu tayar da zaune tsaye a jihar.

Sakataren ya ce gwamnati tana Allah-wadai da irin kashe-kashen da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke yi a wasu sassan jihar, lamarin da ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ga bayansu.

Kazalika, Matane ya ce gwamnati ba ta manta da halin da wadannan matakai za su jefa al’ummar jihar ba, sai dai ya ce an dauke su ne da manufar tsare rayuka da dukiyoyin al’umma, inda ya yi kira ga dillalan babura a fadin jihar da su bai wa gwamnatin hadin kai.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su bai wa gwamnati da sauran hukumomin tsaro hadin kai a yayin da babu dare babu rana suke fadi-tashin ganin an kawo karshen ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar.

Sakataren Gwamnatin ya kuma umarci hukumomin tsaro da ke jihar da su tabbatar an kiyaye wannan sabbin matakai da aka shimfida.

Matane ya kuma sake nanata cewa haramcin da aka sanya wa ayyukan ’yan Kabu-Kabu da masu Acaba wanda aka fi sani da Okada na nan daram a birnin Minna da kewaye.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin Jihar Neja ta sanya dokar da ta takaita zirga-zirgar babura masu kafa biyu daga karfe 6 na yamma zuwa na safe.