✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: An bukaci Fulani makiyaya su yi wa dabbobinsu lamba

Mun shirya yin hakan domin kawo karshen matsalar da muke fuskanta.

Masu ruwa da tsaki a al’amuran da suka shafi noma da kiwo na ci gaba da hobbasa wajen samar da mafita ga matsalolin da suka shafi al’ummar Fulani makiyaya.

A makon jiya ne kwararren likitan dabobbi, Dokta Abdulkadir ’Yammama ya kai ziyara a wasu daga cikin rugagen Fulanin makiyaya da ke Kudancin kasar nan.

Likikitan ya shawarce su da su dauki matakin yi wa dabbobinsu lamba ta yadda za a sami ikon kididdiga tare da samar da bayanan dabbobinsu da kuma kowane makiyayi da ke mallakarsu.

’Yammama ya gana da shugabannin Fulani makiyaya na Jihar Ogun a karar shanu ta Randa da ke Abeokuta a ranar Asabar din da ta gabata.

Alfanun yi wa dabbobi lamba

Ya ce ta hanyar kididdigar ne za a san yawan shanun da ke kasar nan, aka kuma san bayanan masu mallakarsu da inda suke zama.

A cewarsa, wannan mataki ne na magance matsalar satar shanu wacce ita ce ummul’aba’isin duk wata matsalar da Fulani makiyaya suka sami kansu a ciki a halin yanzu.

A zantawarsa da Aminiya, ’Yammama ya zayyana muhimmancin samun goyon bayan Fulani makiyaya su yi wa daukacin dabbobinsu lamba.

’Yammama ya ce za a samu damar magance da yawa daga cikin matsalolin da suka shafe su ta fuskar tsaronsu da na dabbobinsu da kuma matsalolin da ke tsakaninsu da manoma.

“Ita wannan lambar akwai na’urar tattara bayanai da ke jikinta wacce take dauke da hoton dabbar da ta mai dabbar da kuma bayanansa, kuma duk inda ta shiga za a gano ta.

“Wannan hanya ce ta magance matsalar satar shanu wacce ita ce musabbabin duk wata matsalar tsaro da ta shafi Fulanin.”

Ya ce, kididdige yawan Fulanin da dabobbinsu zai taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa Fulanin.

Ya ce kowace dabba na bukatar lambar shanun a kunnuwanta biyu, kuma ana sanya wa babbar dabbar a kan Naira dubu biyu, yayin da ake sanya wa karamar dabba akan Naira dubu daya.

Tattaunawa da wadanda lamarin ya shafa

Wakili Inusa Adamu, shi ne Sarkin Fulanin Ogunmakin wanda a baya wasu ’yan bindiga suka kone rugarsu kuma a yanzu suke gudun hijira a wani masallaci a garin Ogunmakin.

Yayin taron wayar wa Fulanin kai a kan lambar shanun, ya ce lalle lambar tana da amfani domin da idonsa ya gani akwai wani babban Soja da ya je da shanu kuma duk shanunsa ya sanya masu wannan lambar.

Ya ce su ma Fulanin makiyaya a shirye suke su yi hakan domin kawo karshen matsalar da suke fuskanta.

Alhaji Yusuf Abubakar, daya daga cikin shugabannin Fulanin makiyaya da ke zaune a Abeokuta cewa ya yi a yanzu ba matsalar lambar shanu ba ce a gabansu ba, ya ce gwamnati ta mayar da Fulanin saniyar ware.