Al’ummar Fulani makiyaya da ke zaune a yankin Ikilala a Shimawa a Ƙaramar Hukumar Shagamu a Jihar Ogun sun koka kan kawar da kai da nuna halin ko-in-kula da ’yan sandan jihar suke nuna musu.
Lamarin na zuwa ne bayan da suka kai musu rahoton wasu mutane suna far masu a yunƙurinsu na tursasa su su bar yankin tare da ƙone rugagensu da dukiyoyinsu da suka haɗa da tufafi da kuɗaɗe da wayoyin hannu.
- Uba ya rasu yana ƙoƙarin belin ’ya’yansa a ofishin ’yan sanda
- Sarki Bamalli ya naɗa ɗansa sabon Walin Zazzau
Shugaban Fulani Makiyayan yankin, Alhaji Ja’afaru Isa, ya shaida wa Aminiya cewa mutanen da suka ƙone masu matsugunin da farko sun kawo masu takarda da lambar waya, cewa su tashi daga wajen, amma da suka sanar da wanda ya ba su wajen sai ya ce su ci gaba da zama, shi ne ya mallaki wajen, kuma shi ne ya sahale masu su zauna.
“Waɗanda suka kawo takardar sun zo ne da rakiyar wani ɗan sanda mai suna Ɗanladi wanda ke aiki a ofishin ’yan sanda na Shimawa, lokacin da mutanen a ƙarƙashin wani da ake kira Shokoto suka nemi mu tashi mu bar wajen cikin mako biyu, sai wannan ɗan sanda mai suna Ɗanladi ya ce su ba mu wata biyu.
“Bayan sun tafi, ƙasa da wannan lokaci sai muka samu labarin mutanen sun zo rugarmu ɗauke da makamai, sun iske matanmu sun kore su sun ƙone bukokkinmu da suturunmu da abincinmu baki ɗaya.
“Ba su bar mana komai ba, sai kayan da ke jikinmu. Na kai ƙara ofishin ’yan sanda wajen DPO, amma sai ya ƙi ya saurare ni.
“Hakan ya sa na wuce zuwa babban ofishin ’yan sanda na Area Command da ke Shagamu.
“A wannan karo Kwamandan yankin ya turo ’yan sanda sun zo sun ga ɓarnar da aka yi mana, sannan ya gayyaci wanda ya jagoranci ƙone mana dukiya, amma abin mamaki sai suka ƙyale shi ya tafi, suka yi watsi da lamarin,” in ji shi.
Fatima Adamu, ɗaya daga cikin Fulanin da aka ƙone wa dukiya ta ce a lokacin da maharan suka isa rugarsu tana da kuɗin saniyar ta da ta sayar Naira 300,000.
Ta ce tana zargin ko dai maharan sun sace kuɗin sun tafi da su, ko kuma sun ƙone su a ɗakin da ta ajiye su.
Haka kayan auren ’yarta da ake shirin yi duk sun ƙone bayan sun ɗebi wasu sun tafi da su.
“A lokacin da suka kawo mana harin akwai mata masu ciki su biyu sai da suka haihu a lokacin cikin zullumi.
“Sun haihu a lokacin da aka ƙone mana matsuguni haka ruwa ya sauka kan masu jegon da jariransu.
“Yanzu haka suna fama da rashin lafiya duk jikinsu ya kumbura kuma ba mu da kuɗin da za mu kai su asibiti,” in ji ta.
Aminiya ta tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun Omolola Odutola, wacce ta ce ba ta da masaniya kan faruwar lamarin, ta kuma ta ce babban jami’in ’yan sandan yankin ba ya gari.
Sai dai ta ce Fulani makiyayan suna zaune ne a wurin ba bisa ƙa’ida ba, kuma irin wannan zaman shi ke haifar da ɓatagari.
Fulani makiyayan sun sun ce suna zaune ne da sanin mai wajen, wani mai suna Emmanuel wanda ya sahale masu zama a wajen, har ma ya katange masu wajen.
Don haka suke neman hukumomi su taimaka su shiga lamarin a bi musu haƙƙinsu.