✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: A Rika Gaggawar Kai Rahoton Bata-Gari —Sarkin Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya umarci masu unguwanni da su rika kai rahoton bata-gari ga hukuma cikin gaggawa don daukar matakin da ya dace.…

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya umarci masu unguwanni da su rika kai rahoton bata-gari ga hukuma cikin gaggawa don daukar matakin da ya dace.

Sarkin ya fadi haka ne a fadarsa a lokacin da ya ke karbar rahotanni daga masu unguwanni da dagatai a wani zama na fada a ranar Laraba.

Sarkin ya bayar da umarnin ne ta bakin Wazirin Kano Alhaji Sa’ad Shehu Gidado bayan ya saurari rahoton kisan wani yaro dan shekara uku da wani matashi mai shekara 22 ya yi a yankin ’yan mata da ke unguwar Bachirawa.

Sarkin yana mai cewa, “A rika kai rahoton matasan da ake shaye-shaye da duk wani mummunan hali ga dagatai da hakimai da kuma hukumomin tsaro don daukar matakin da ya dace, kar a jira sai an aikata laifi tukunna”.

Dagacin ’Yan Mata, Muhammad Lawal Abdulkarim, ne ya bayar da rahoton cewa wani mai matashi ya halaka wani yaro mai suna Aliyu Nura mai shekara uku a farkon makon nan.

Mahaifin yaron Malam Nura Lawan ya yi karin bayani ga sarki yadda abin ya faru, sannan ya ce an kama wanda ake ke zargi kuma a yanzu maganar na hannun hukumar ’yan sanda ta jihar.