Ko me ke kawo mutum ya ji idan ya tashi daga barci, gabobinsa da namomin jikinsa, kamar na kafa ko hannuwa, suna ciwo kamar ana dandatsawa?
Daga Yusuf, Zaria
Amsa: Wannan bayani yana kama da tsamin jiki (tsami na ciwo da gajiya, ba na wari ba), abin da muke kira ‘lactic acidosis’. Idan mutum ya motsa jiki da ya wuce kima ko ya yi aikin karfin da ya wuce misali, naman jikinsa zai shanye duk wata iskar ‘odygen’ da dan abincin da aka tara a cikin naman. To idan ya kwanta barci, namomin cikin jikin nasa sukan saki wasu sinadarai na ‘lactic acid’, masu kawo tsamin jiki. Banda wannan, akwai rashin lafiyar ma da za ta iya sa mutum ya rika jin irin wannan, kamar karancin jini misali. Akwai kuma kwayoyi da za su iya sa hakan, har ila yau.
Wannan na faruwa ne saboda su gabobin ba su samu isasshiyar iskar ‘odygen’ da abinci ba, a yayin da suke aikin karfin. An fi yawan samun irin wannan a wurin ’yan wasa, kamar na kwallo ko na gudu, abin da suke kira ‘fatigue’; ko a wurin ’yan dako wato masu sana’ar daukar kayan nauyi. A wasu lokuta, wanda aka yi wa dukan kawo-wuka kan samu irin wannan, gami da taruwar jini a namomin da aka doka.
Idan mutum yana yawan samun irin wannan, yana nufin ba ya cin isasshe ko lafiyayyen abincin da ya kamata, kafin ya yi irin wannan aikin karfin. A likitance, an ce a rika motsa jiki a kalla na mintuna ashirin zuwa talatin a rana, to amma da zarar wannan motsa jiki ya fara wuce awa daya ba tare da an huta ba, to fa irin wannan ce za ta rika faruwa, don jiki ba inji ba ne. Shi ya sa, a ka’ida, babu wasan da yake kaiwa awa guda ba tare da an samu an huta na dan wani tsawon lokaci ba. Wannan ce kuma kan sa wasu samari shan kayan maye da sunan wai karin kuzari. Duk abin da aka sha, in dai ba sinadarin suga ba ne a ciki, to bata lokaci kawai aka yi.
A lokuta da dama akan samu masu irin wannan motsa jiki da ya wuce misali, a ga haka kawai sun yanke jiki sun fadi saboda karewar kuzari. A da dai mun san a filin wasanni, musamman a makarantu, malaman koyar da motsa jiki sukan kunshe sinadaran magunguna da dama a jakunkunan kar-ta-kwana (wato first-aid kit). Akan kunshe kamar sinadarin Glucose-D wato bulkodi da lilimen da maganin wanke ciwo da plaster da auduga da sauransu, amma ba mu sani ba, ko har yanzu ana ajiye irin wadannan a filayen wasanni. Haka nan a yanzu mutum zai ga samari, wadanda ba su da cikakkiyar koshin lafiya, a ido, sun zage suna ta kwallo fiye da awa ba hutawa, masu kosasshiyar lafiya kuma sun taru a gefe suna kallonsu! Wato dai kusan ba wadanda ya kamata su motsa jikin ne ma suke motsawa ba.
Sai dai ita wannan matsala ta tsamin jiki ba ta bukatar wani magani, illa dan hutun kwana daya zuwa biyu. Wato ba wani magani da aka sani da zai narkar da wannan sinadarin ‘acid’, idan ya riga ya taru, sai dai kawai mutum ya dan huta na kwana biyu kuma ya rika wanka da ruwan dimi mai dan zafi sosai da sawa a danna masa wurin, wato tausa, har abin ya baje. Idan mutum yana irin wadannan wasanni na wuce misali ko yana aikin dako, zai iya sayen kayan kara kuzari kamar bulkodi ko lukozed ko dan wani lemon kwalba (don dukansu dai suga ne cikinsu mai saurin bin jiki) ya dan sha kadan tsakanin hutun rabin lokaci don kiyaye aukuwar tsamin jiki.
SAURAN TAMBAYOYI
Wai yawan shan kwayoyi masu gusar da hankali zai iya jawo wa mutum ciwon farfadiya?
Daga Zahraddeen
Amsa: E! Duk abin da zai shiga kwakwalwa ya yi aikin da ya wuce kima, kamar yadda kwayoyin maye suke yi, zai iya rikita aikin kwakwalwar. Idan hakan ta faru, ana iya samun komai tun daga farfadiya har zuwa hauka.
Wai yawan shan ‘turamal’ yana iya kawo wa namiji rashin haihuwa?
Daga dan Gezawa
Amsa: A’a! Bayanai sun nuna aikin wannan kwaya a kwakwalwa yake, don haka sai dai ta rikita aikin kwakwalwa.
Ina amfani da tabaron ido. Matsalata a yanzu, idan na dade ina kallon abu, sai na fara gani dishi-dishi. Me ke sa min haka?
Daga Mustapha H., Kano
Amsa: Waccan matsala da ta sa aka yi maka tabarau, watakila ita ce dai ta sake ta’azzara, wato sai ka koma ke nan an sake auna karfin idon, an sake saisaita maka karfin ruwan gilashin. Haka nan kuma za ta iya yiwuwa wata sabuwar matsala ce daban, wadda ba ta ma shafi shi wannan gilashi naka ba.
Me ke kawo ciwon ido da jin kamar kaikayi a cikin idon?
Daga Adamu dankasuwa
Amsa: Matsalolin ido yawa gare su, amma wadda ta fi kawo irin wannan ba ta wuce gilakoma. Ko ma dai mene ne, mai wannan matsala yana bukatar ganin likitan ido.
Idan ina barci miyau na yawan taruwa a bakina. Na je wurin likita an a’auna ni an ce kalau nake. Ina neman shawara.
Daga Muttaka Yunus
Amsa: Ai kusan kowa idan yana barci miyau na taruwa a bakinsa, na wasu ma har gangarowa yake kan matashi. Idan kana tsabtace bakinka da kayan goge baki kafin kwanciya, miyau ba zai rika yin yawa ba, kuma ba za ka ji kyamar hadiyewa ba, idan ma ya tarun.
Ko cin yaji a kullum, wanda aka daka da ka-fi-zabo zai iya kawo illa?
Daga Malam Malam, Gololo
Amsa: E, kwarai kuwa! Tunda a abincin da za ka sa yajin ma watakila akwai gishiri da ka-fi-zabuwa, sa’annan kuma yajin ba a dafa ba, ta yadda dafuwar za ta rage karfin ka-fi-zabuwar. Da kamar a ce a abincin da za ka sa yajin ba magi ba gishiri, kamar danwake, to ba damuwa, amma a mafi yawan lokaci a abincin da aka riga aka sa wa magi mutane suke karawa. Don haka saka yajin da aka daka haka zalla a abinci zai fi lafiya, tunda shi kanshi barkono akwai bitaman na rukunin C a ciki.
LAFIYAR MATA DA YARA
Sinadaran da Mai Juna Biyu Ta Fi Bukata
Duk da irin magunguna da ake ba mai juna biyu idan ta je awo, ba dole ba ne a ce su magungunan su kara wa mace sinadaran da take bukata yadda ake so, domin muna da sanin cewa ba kowace mace ke son shan wadannan kwayoyi ba. Wasunsu sukan manta, wasu kuma su ce kwayoyin na sa su amai.
Dole ne maigida ya shigo ciki ya taimaka ta hanyar cefane mai kauri idan uwargida ta samu juna biyu.
Ga sinadaran da mace mai juna biyu ta fi bukata:
1. Sinadarin Iron: Wannan sinadari shi ne ke da alhakin sarrafa kwayoyin jini, wanda karancinsa kan faru a kowace mai juna biyu. Alamun karancin jini a jiki sun hada da yawan gajiya, yawan faduwar gaba da yawan samun ciwon kai. Ana samun wannan sinadari a nama, hanta, alayyahu, wake da waken soya. Duk da wanda za a samu a abinci, dole a hada da na kwaya na asibiti, wasu jajayen kwayoyi. Idan ba za a iya hadiya ba, akwai na ruwa, sai dai mata suna korafin na ruwan yana karni.
2. Sinadarin Folic acid: Wannan sinadari shi ne ke da alhakin kyautata ingancin dukkan kananan halittun jiki (wato cells). Ana samunsa da dama a hanta, kwai, da kayan ganye, wake da kayan marmari. Ana so matar da take da niyyar samun juna biyu dole ta nemo kuma ta fara shan kwayoyin wannan sinadari tun ma kafin ta samu juna biyu. Wato ba kamar sinadarin iron ba, wanda akan fara sha daga wata uku da samun juna biyu, shi sinadarin ‘folic acid’ tun ana amarci mace take fara sha duk da cewa tana samu a abinci. Wannan sinadari yakan rage haihuwar jarirai masu nakasa a jiki, kamar masu yankakken lebe, ko masu cindo, ko masu wata nakasa a gadon baya da dai sauransu.
3. Sinadarin Calcium: Wannan yakan taimaka wa jariri wajen gina kasusuwa masu kwari, kuma ana samunsu a madara, da kifi. Akwai ma wasu nau’ukan abincinmu da yanzu akan kara wa wannan sinadari. Ana so mace mai juna biyu ta rika yawan cin wadannan.
4. Sinadarin bitaman na rukunin D: Shi ma wannan ba a ba da shi a asibiti don haka ne za a nemo shi a abinci. Shi ma akan iya samunsa a kifi da madara. Akwai wanda kuma jikinmu ke sarrafawa daga hasken rana a karkashin fatarmu. Shi ma wannan sinadari dole ne a samu a rika sha domin yakan taimaka wa sinadarin ‘calcium’ ne wajen samun kwarin kashi da hakora.
Haka nan ko da mace ta haihu bai kamata ta daina shan wadannan kwayoyi ba ko abinci masu wadannan sinadarai, har sai yaro ya yi kwari sosai.