Sakamakon matsalar tsaron da ta addabi Jihar Katsina, Gwamnatin Jihar ta haramta zirga-zirgar ababen hawa a hanyar da ta tashi daga Jibiya zuwa Gurbin Baure har sai abin da hali ya yi.
Dokar ta kuma shawarci duk masu bin hanyar da su yi amfani da hanyar Funtuwa.
- Iran da Saudiyya za su koma tattaunawar gaba-gadi
- e-Naira: Abubuwa 9 da ya kamata ku sani a kan sabon kudin intanet
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sabuwar doka da Gwamnan Jihar, Aminu Bello ya sanya wa hannu ranar Talata.
Kazalika, dokar ta haramta wa motocin haya bin hanyar Kankara zuwa Sheme, amma masu motocin kansu zasu iya bin hanyar.
Gwamnatin ta kuma haramta wa manyan motoci daukar itace daga dukkan dazukan Jihar tare da haramta sayar da dabbobi a kasuwannin Kananan Hukumomin Jibia da Batsari da Safana da Charanchi da Mai’adua da Malumfashi da Kafur da Sabuwa da Kankara da Faskari da Baure da Danmusa da Dutsinma da Kaita.
Dokar dai za ta fara aiki ne daga ranar Talata, 31 ga watan Agustan 2021.
Gwamnatin ta kuma haramta jigilar dabbobi a manyan motoci zuwa sassan kasar nan daga Jihar da kuma daukar mutum uku a kan babur ko kuma sama da mutum uku a motar Kurkura a fadin Jihar.
Bugu da kari, daga yanzu an hana sayar da tsofaffin babura a kasuwar Charanchi.
“Dokar ta sake jaddada hana hawa Babur daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe, da kuma 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a Kananan Hukumomin da matsalar rashin tsaron ta fi addaba.
“Dokar ta kara jaddada haramci sayar da man Fetur a cikin jarka. Gidajen mai biyu kadai gwamnati ta amince su rika sayar da man a Kananan Hukumomin da matsalar rashin tsaro tafi addaba kuma ba za a sayar wa mutum man da ya wuce na N5,000 ba,” inji sabuwar dokar.
Sai dai gwamnatin ta kebe ma’aikatan lafiya jami’an tsaro da ’yan jarida da cewa za su iya yin amfani da babur mai kafa biyu ko mai kafa uku a wuraren da aka kafa dokar.