Majalisar Wakilai ta nemi gwamnatin Shugaba Buhari ta ayyana dokar ta-baci kan aikata kashe-kashe don yin tsafi a fadin kasar.
Kiran na cikin kudirorin da wakilan suka cimma a zamansu na ranar Laraba bayan gabatar da wani kudirin gaggawa kan rayuwar jama’a mai taken ‘Need to Curb the Rising Trend of Ritual Killings in Nigeria’ – bukatar dakile kisan gilla don aikata tsafi a Najeriya.
- Matsalar tsaro: Fintiri ya hana hawa babura a kananan hukumomi 2
- ’Yan bindiga sun kashe DPO da soja a Katsina
Shugaban Marasa Rinjaye Toby Okechukwu ne ya gabatar da kudirin, inda ya bayyana damuwa kan yadda ake sace-sacen mutane da yi wa wasunsu fyade, sannan a wasu lokutan bayan kashe a yanki sassan jikinsu domin aikata tsafi.
Ya hikaito yadda wani bincike na Hukumar Agaji ta Red Cross ya bayyana cewa an samu rahoton yadda kimanin mutum 10,480 suka bata a fadin Najeriya a shekarar 2017..
Majalisar ta bayyana damuwa kan matsalar a yayin da ake samun rahotannin kisan gilla da zummar neman kudi ta hanyar tsafi a sassan Najeriya, inda na baya-bayan nan shi ne wanda aka kashe wata Sofiat Kehinde a Jihar Ogun sannan aka tafasa kokon kanta a cikin tukunyar girki.
’Yan majalisar sun yi kira ga Hukumar Wayar da kai ta Kasa National Orientation Agency (NOA) da iyaye da shugabannin makarantu da malaman addini da ’yan jarida da su fara kamfe don dakile ci gaba da faruwar kashe-kashen.