Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa kwamiti domin binciken wasu kudin jihar Naira biliyan 107 da ta zargi gwamnatin da ta gabata da yin awon gaba da su.
Kafar watsa labarai ta Premium Times ta wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Jihar, Zailani Bappa tana cewa Mataimakin Gwamnan Jihar, Alhaji Mahdi Aliyu Gusau ne ya bayyana matsayin gwamnatin bayan zaman Majalisar Zartaswar Jihar.
Alhaji Mahdi Aliyu ya ce, wannan shawara ce da kwamitin da aka kafa tun farkon hawan gwamnatinsu domin ya binciki yadda tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ya kashe kudaden jihar.
Ya ce an gano wasu kudade har Naira biliyan 107 da suka bace, ba a san yadda aka yi da su ba.
“An gano Naira biliyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta zuba a asusun gwamnatin jihar, ta hanyar Intanet, amma cikin kwana biyu aka neme su aka rasa kuma ba su shiga asusun jihar ba.”
“Sannan an gano wasu Naira biliyan 10 da aka saka cikin asusun wasu kamfanonin ’yan canji a Kano.
“Wadannan kudade kamata ya yi su shiga asusun gwamnatin jihar amma aka karkartar da su.”
“Sannan da wasu harkalla masu yawa na biliyoyin Naira da suka bace babu su,” inji shi.
Ya ce wannan bincike ya zama dole saboda amanar da mutanen Jihar Zamfara suka ba shi.
Ya ce ba zai saka ido ya bari a barnatar da kudaden talakawan jihar ba sannan bai yi komai a kai ba.
Sai dai Kakakin tsohon Gwamna Yari ya ce ba su tsoron wannan kwamiti saboda ba su aikata abin da ake zarginsu da aikatawa ba.
“Ba gudu ba ja da baya, muna jiransu,” inji shi.