✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Matawalle ya sauya sheka daga PDP zuwa APC’

Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, kamar yadda hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad ya bayyana.

Da ma dai Aminiya ta rawaito yadda gwamnan ya fara shirye-shiryen sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP.

  1. Wankan kududdufi ya yi ajalin dan shekara 14 a Kano
  2. Yadda aka hana iyayen daliban Islamiyyar Tegina hira da ’yan jarida

A shafinsa na Facebook, Bashir Ahmad ya wallafa cewa, “Zamfara ta dawo gida, barka da zuwa Matawalle.”

Mako biyu da suka gabata, wani jigo a Gwamnatin Zamfara ya shaida wa Aminiya cewa Gwamna Matawalle zai koma jam’iyyar APC kafin karshen watan Yuni, 2020.

Har yanzu Gwamna Matawalle bai ce uffan ba game da ficewarsa daga PDP, amma alamu sun nuna yana shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar.

Wani jigo a jam’iyyar ya ce an kammala shirye-shiryen bikin karbar Matawalle a APC ranar Talata mai zuwa.

Bikin Karbarsa

“A ranar Talata za a gudanar da taron karbar Gwamna Matawalle zuwa APC a Gusau,” a cewar majiyar.

Tuni gwamnan na Zamfara ya shiga yi wa tarukan PDP a sha ruwan tsuntsaye.

Mako biyu da suka gabata ne gwamnan ya kaurace wa taron da PDP ta yi a Uyo , babban birnin jihar Akwa Ibom, inda ya tura mataimakinsa don ya wakilce shi.

Kazalika, lokacin da jam’iyyar ta yi bikin karbar tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke, daga jam’iyyar, Matawalle ya sake tura mataimakinsa a matsayin wakilinsa.