✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matawalle ya sauke basarake kan ba wa soja mai sayar da makamai sarauta

An kama sojan a yayin da yake kokarin mika makamai ga ’yan bindiga

Gwamnan Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya dakatar da wani basarake da ya ba da sarauta ga wani soja da aka kama yana sayar wa ’yan bindiga makamai.

An kama sojan ne da harsasan da yake kokarin mikawa ga wani dan bindiga a kauyen Maniya a Masarautar Shinkafi, bayan ya karbi kafin alkalamin N100,000 a hannun ’yan bindiga.

Yayin dakatarwar da Hakimin Badarawa na Masarautar Shinkafi, Surajo Namakkah, Matawalle ya ce ba zai raga wa masu yin kafar ungulu ga kokarin gwamnain jihar na kawo zaman lafiya ba.

Gwamnan ta bakin kakakin gwamantin jihar, Yusuf Idris, ya ce dakatarwar ta sai abin da hali ya yi ne, kuma ta fara aiki ne daga ranar Juma’a sannan ya  wajabta neman amincewar Gwamantin Jihar kafin a ba da sarautar gargajiya.

Matawalle ya kuma yaba wa jami’an tsaro da suka kama wani mai suna Dokta Kamarawa wanda ke samar wa ’yan bindiga kayan soja da magunguna a Jihar wanda aka kama shi da kaki da katuna shaidan soja.

Matawalle ya bayyana takaicinsa kan yadda bata-garin jami’an tsaro ke taimaka wa ayyukan ’yan bindiga, abin da ya ce babbar barazana ce ga kokarin kawo karshen matsalar tsaro.