Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya rantsar da sabbin manyan sakatarori shida domin cike gibin da ke akwai a shugabancin ma’aikatun gwamnatin jihar.
Bayanin nadin na kunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta hannun Sakataren Yada Labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu a ranar Juma’a a Gusau, babban birnin jihar.
- Yadda soja ya kashe abokan aikinsa a Borno
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dan Chana Ya ce Ya Kashewa Ummita Miliyan N120
Rantsarwar ta shafi har da wasu masu bai wa gwamana shawara na musamman su hudu hadi da babban jami’in binciken harkokin kananan hukumomin jihar da sauransu.
Da yake jawabi yayin rantsawar a fadar gwamnatin jihar, Matawalle ya yi kira gare su da su yi amfani da kwarewarsu wajen gudanar da tsare-tsaren gwamnati.
Kana ya nusar da manyan sakatarorin game da ayyukan da suka rataya a kansu dangane da ma’aikatun da za su jagoranta.
Matawalle ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci aikata ba daidai ba ko kuma yi wa doka karan tsaye.