Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle ya kalubalanci malaman Jihar da su gayyato Sheik Ahmad Mahmud Gumi domin ya fadada yawon da’awarsa zuwa Jihar Zamfara domin yi wa ’yan bindiga wa’azi su tuba su daina miyagun ayyuka.
Gwamna Matawalle ya bayyana haka ne yayin wani taron gaggawa da aka shirya kan zaman lafiya a Jihar Zamfara da ya hada da Malamai da sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaron Jihar a birnin Gusau.
- Mutum 3 sun gurfana a gaban kotu kan laifin tayar da zaune tsaye
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
Ya bukaci da su gayyato Sheik Gumi, su fada masa cewa ya fadada manufarsa ta wa’azantar da ‘yan bindigar zuwa Jihar Zamfara a matsayinsa na dan asalin Jihar duba da bukatar da ake da ita na samar da zaman lafiya a Jihar.
“Muna da malamanmu, muna sane da cewa suma za su iya makamancin wannan kokarin, amma ina bukatarsu da su fadada dabarun yadda za a shawo kan lamarin. Fatan mu dawo da zaman lafiya a Jihar,”a cewar Gwamna Matawalle.
“Akwai wani lokaci da na kira daya daga cikin malamai a Gusau, Sheik Umar Kanoma da daddare, suka tattauna da wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka tuba, suka amince za su ajiye makamansu,” inji shi.