Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara, ya amince da dakatar da Aliyu Tukur a matsayin Kwamishina a Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta jihar.
An soke nadin nasa ne biyo bayan tabbatar da sa hannunsa cikin ayyukan da za su iya bata sunan gwamnatin Jihar Zamfara kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ya sanya wa hannu.
- Wa’adin amfani da tsoffin kudi ya cika —CBN
- Matawalle ya kori kungiyoyi masu zaman kansu daga Zamfara
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a kwanakin baya an gurfanar da kwamishinan a gaban kotu bisa wasu ayyukan zagon kasa da ka iya zubar da kimar Gwamnatin Gwamna Bello Matawalle.
An bukaci tsohon kwamishinan da ya mika duk wasu takardu da kadarorin gwamnatin da ke hannunsa ga Babban Sakataren ma’aikatarsa.
Wannan na zuwa ne biyo umarnin da gwamnan ya bayar na korar kungiyoyi masu zaman kansu a fadin jihar.
Gwamnatin jihar ta ce ta gano wasu daga cikin kungiyoyin da hannu wajen rura wutar matsalar rashin tsaro a jihar da makotanta.