✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matawalle ya fallasa masu hannu a sace Daliban Jangebe —NEF

Ya kamata Gwamnan Zamfara ya fallasa mutanen da ke da hannu a sace dalibai 279 a Jangebe

Dattawan Arewacin Najeriya sun bukaci Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya gaggauta bayyana sunayen wadanda suka sace dalibai mata 279 a makarantar karamar sakandaren GGSS Jangebe da Jiharsa.

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta ce ba yadda za a yi Gwamnan ya yi zargi mai “karfi da daure kai” kan masu hannu ba sace daliban ba tare da ya ba hujjoji ba ga hukumomin tsaro.

Kafin a sako daliban, Matawalle ya ce idan aka bayyana wa ‘yan Najeriya su wa suka sace ‘yan matan, sai abin ya daure musu kai.

Bayan sako su kuma gwamnan ya ce a lokacin da gwamnati ke tattaunawa da masu garkuwar kan sako daliban, mutanen da ya zarga sun zaga suna wa ‘yan bindigar tayin kudi cewa kar su sake su.

A zantawarsa da Aminiya kan hakan, kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce ba yadda za a yi gwamnan ya yi zargi mai karfi haka ba tare da kwarara hujjoji ba ga hukumomin tsaro.

“Sai dai idan hukumomin gwamnati yake zargi da hannu a garkuwa da kuma yin kutungwila ga kokarin ceto daliban,” inji shi.

Ya ce duk da cewa dattawan Arewa na farin ciki cewa yaran sun kubuta, sun damu da aka siyasantar da lamarin.

Baba-Ahmed ya ce ce-ce-ku-ce da shugabannin ke yi kan batun na iya ba wa masu garkuwar kwarin gwiwa.

Ya ce shi ya sa ko a baya kungiyar ta gargadi gwamnoni a matsayinsu na shugabanni su rika taka-tsantsan idan za su yi magana.