Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin bude layukan sadarwa a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Zailani Bappah, mashawarci na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da jama’a, ya nakalto Gwamna Matawalle yana cewa ya kamata a bude layukan sadarwa daga ranar Juma’a.
- Ana cikin tasku saboda karancin man fetur a Landan
- Coronavirus: Karin mutum 19 sun mutu a jihohi 12 — NCDC
Hakan na zuwa bayan fiye da makonni uku da aka toshe hanyoyin sadarwa da intanet a fadin Zamfara, matakin da hukumomi suka ce sun dauka domin kokarin magance matsalolin ’yan bindiga masu kai hare-hare da satar mutane a jihar
A cewar Zailani, “Gwamnan ya bayar da umarnin dawo da hanyoyin sadarwa a cikin birnin Gusau kadai daga ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoban 2021.
“Maido da hanyoyin sadarwa a babban birnin jihar ya zama tilas bayan gagarumar nasarar da aka samu wajen yaki da yan fashin daji a jihar.
“Sannan kuma an yi hakan ne domin rage radadin wahalar da gwamnati da sauran bangarori masu zaman kansu suka fuskanta musamman a kan sha’anin harkokin kasuwanci.
“Gwamnati ta ga ya zama wajibi ta saukaka tsaurin da ta yi kan matakan da ta dauka bayan nasarar da aka samu na ragargaza dukkan wasu miyagu da sauran ababe na ta’addanci da suka hana ruwa gudu a jihar.
Gwamna Matawalle ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa kuma a nan gaba za ta sanar da shawarar da ta dauka bisa la’akari da tsayuwa a kan tubali na daidai.