Matatar Man Fetur ta Warri da ke Jihar Delta, ta fara aiki bayan shafe shekara tara a rufe.
Matatar, wadda aka dakatar da aikinta a shekarar 2015 saboda gyare-gyare, ta ci gaba da aiki, inda aka fara tace man fetur.
- ’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos
- Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda
Wannan zai rage dogaro da man fetur da ake shigo da shi ƙasashen waje da kuma bunƙasa harkar mai da iskar gas a Najeriya.
Wani jami’i daga Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabbatar da cewa matatar yanzu haka tana tace man dizel, kalanzir da sauransu.
Amma man fetur da iskar gas, har yanzu bai fara aiki ba.
“An fara aiki, amma ba a sanar da hukumomi ba tukuna. A halin yanzu ɓangare ɗaya ne ke aiki, yayin da muke jiran sauran sassa, ciki har da FCC, su fara aiki,” in ji wata majiya.
Ana sa ran ɓangaren FCC zai fara aiki mako mai zuwa, wanda zai ba da damar samar da man fetur da sauran muhimman kayayyaki.
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, zai ziyarci matatar a ranar Lahadi, domin ganin yadda aiki ke gudana.
An kuma ƙara tsaurara matakan tsaro a kusa da matatar, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Duk da cewar fara aiki matatar babban ci gaba ne, amma jama’a na jiran ganin yadda mai zai samu a matatar.
Ƙoƙarin jin ta bakin jami’an WRPC da NNPCL bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.