✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matatar Man Fatakwal ta fara aikin gwaji

Matatar Man Fatakwal ta dade ba ta aiki kamar sauran matatun mai da gwamantin Najeriya ta jima tana kashe kudin domin farfaɗo da su

Matatar Mai Ta Fatakwal ta fara aikin gwaji bayan shafe shekaru ba ta aiki, duk da kudaden da Gwamnatin Tarayya ta yi ta kashewa domin farfaɗo da ita.

Matatar Mai ta Fatakwal, kamar sauran da gwamantin Najeriya ta jima tana kashe kudin domin farfaɗo da su, ta tashi ne bayan aikin gyaran ta da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta bayar.

Rahotanni sun nuna a safiyar Alhamis ne aka ga matatar mai karfin tace ganga 210 na danyen mai a kullum ta fara aiki.

Haka lya sa ’yan Najeriya suka shiga rige-rigen yada albishir din a kafofin sada zumunta cewa matatar ta fara aiki.

Kawo yanzu dai gwamnati ba ta ce komai gane da lamarin ba.

Amma tsohon Shugaban Kungiyar Dillalan Mai Na Najeriya (IPMAN) a Jihar Ribas, Joseph Obele, ya shaida wa wakilinmu cewa kashi an kammala kashin farko na gyaran matatar man, kuma an fara aikin gwaji.

Obele wanda a zamaninsa yake jagorantar kwamitin sanya ido kan gyaran matatar ya shaida wa wakilinmu da ya tambaye shi inda aka kwana a gaura matatar cewa “Ana ci gaba da gwajin.”

A baya dai an yi ta ce-ce-ku-ce bayan da masu ruwa da tsaki suka bayyana shakka game da yiwuwar kammala aikin gyaran matatar a watan Disambar nan.

A wata ziyarar gani da ido da ya kai matatar, Karamin Ministan Man Fetur,  Heineken Lokpobiri had ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwa za a kammala kashin farko na aiki a cikin watan Disambar.