✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashiya ta sha guba saboda saurayinta ya rabu da ita a Kano

Mahaifiyarta ta ce wannan shi ne karo na biyu da take yunkurin kashe kanta

Wata matashiya mai shekara 24 duniya da ke unguwar Sabuwar Gandu a birnin Kano, ta yi yunkurin shan guba don ta kashe kanta saboda saurayinta ya fasa aurenta.

An ceto matashiyar, mai suna Aisha Ibrahim, ne bayan samun kiran agaji da rundunar ’yan sandan Kano ta yi.

“Bayan samun kiran, nan take muka aike da dakarunmu wurin inda aka ceto rayuwarta. An kai ta asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano sannan aka kwace shinkafar beran da ta yi yunkurin amfani da ita,” cewar kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Matashiyar ta bayyana cewar ba za ta iya rayuwa babu saurayin nata, bayan ya juya mata baya.

“Na sayo shinkafar bera da nufin na ci saboda ba zan iya jurar ganin yana rayuwarsa tare da wasu matan ba, gara na mutu, na gaji da wannan duniyar.

“Ina matukar kaunarsa wanda hakan ne ya sa na zabe shi a matsayin wanda zan aura amma ban san cewar yaudarata yake yi ba. Maganar gaskiya ba zan yafe masa ba,” kamar yadda ta bayyana.

‘Wannan ne karo na biyu tana yunkurin hallaka kanta’

Mahaifiyar matashiyar da aka sakaya sunanta, ta ce wannan shi ne karo na biyu da ’yar tata ke yunkurin halaka kanta.

“Akwai lokacin da ta taba yin irin haka ta sha sinadari Hypo aka ba ta madara. Wannan karon kuma ’yan sanda sun ceto ta bayan ta sha shinkafar bera. Ban taba tsammanin za ta sake aikata irin wannan abu ba wai da sunan soyayya,” inji mahaifiyar tata.

Kazalika, kakakin ’yan sandan ya ce an fara bincike don gano hakikanin abin da ya sa take kokarin shekawa lahira.

Kakakin ya gargadi jama’ar gari da su kiyayi yunkurin kashe kansu, yana mai cewar duk wanda aka kama za a mika shi zuwa kotu don yanke masa hukunci.