✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashiya ta maka mahaifinta a kotu saboda ya yi mata auren dole

Mahafin ya ce ta bar gida tun daga ranar da aka shirya daura mata aure.

Wata matashiya mai shekara 25 ta maka mahaifinta a wata kotu da ke zama a unguwar Rigasa a Jihar Kaduna saboda ya yi mata auren dole.

Matashiyar ta yi karar mahaifin nata ne tana zargin shi da yi mata auren dole har sau uku, a cikin mazajen kuma har da wanda ba ta sani ba.

“Mahaifina ya aurar da ni ga wanda ba na so, ban kuma san shi ba — auren farko da na biyu duk auren dole mahaifina ya yi min.

“Ba zan iya ci gaba da zama ba gaskiya. Ina son kotu ta raba wannan auren”, inji ta.

Ta kara da bayyana wa kotun cewa yanzu haka tana aure a Unguwar Sarki da ke Kaduna.

Da yake jawabi a gaban kotun, mahaifin matashiyar ya ce da farko ta gabatar masa da wani wanda take son ta aura amma daga baya ta ce ta fasa.

“Maganar cewa ba ta son wanda za ta aura ba gaskiya ba ce.

‘Ban san inda ta shiga ba. Ta bar gida tun ranar da za a daura mata aure.

“Ina rokon kotu ta umarce ta ta dawo gida,” inji mahaifinta.

Alkalin kotun Malam Salisu Abubakar Tureta, bai amince da rokon mahaifin nata ba, amma ya umarce ta zauna bisa kariyar kotun sannan ya dage zaman kotun zuwa ranar 10 ga watan Maris, 2022.