Tsohon da wasan kungiyar kwallon kafa ta Jigawa United, Hadi Bala, wanda ke wasa a kungiyar CD Madridejo ta kasar Spain, ya yanke jiki ya fadi ana tsaka da wasa.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce ya rasu ne da yammacin Lahadi, lokacin da suke wasa da kungiyar SP Cabanillas.
- Girgizar kasar Turkiyya: Yawan matattu ya haura 1,900
- Masu POS na cajin N3,000 kan kowace N10,000 da aka cire a wajensu a Anambra
Sanarwar ta ce matashin ya yi mutuwar fuju’a ne a minti na 39 da fara wasa.
A cewar sanarwar, ma’aikatan lafiyar da ke filin wasa na birnin Toledo sun kawo masa dauki, amma daga bisani aka gano ya rasu.
Da yake zantawa da Aminiya, a Kafanchan, dan uwan mamaci Hadi Bala, Misbahu Ado Bala, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Najeriya da duniyar kwallon kafa.
Matashin, mai shekara 21 ya fara wasan kwallon kafa ne da kungiyar Arewa United.
Daga bisani kuma ya buga wa kungiyoyi irin su Shareef Academy da Golden Balley da Zaria Bees da kuma Salama FC dukkan su a Kafanchan.
Daga bisani dai ya koma buga wasa a kungiyoyin kwallon kafa na jihohin Filato da Jigawa.