Aminu Adamu, matashin nan da kotu ta tsare a gidan yari kwanakin baya kan tsokanar matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ya kammala jami’a.
A ranar Juma’a hotunan Aminu na kammala jabarar karshe a matakin digirin farko a Fannin Kula da Muhalli a Jami’ar Alkalam da ke Jihar Katsina suka fita, kimanin mako biyu bayan an sako shi daga gidan yari.
- #FreeAminu: NANS ta kira zanga-zangar adawa da Aisha Buhari
- Ra’ayi: Soshiyal Midiya a Arewa: Aisha Buhari da Aminu Adamu, daga Aliyu Tilde
A makonnin baya ne jami’an tsaro suka gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin cin zarafin Aisha Buhari ta shafinsa na Twitter.
Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da suka ga matar shugaban kasar da ma hukumomin tsaron, tare da zanga-zanga daga Kungiyar Daliban Najeriya da suka nemi a gaggauta sakin sa.
Bayan kotu ta ba da umarnin tsare shi a gidan yari, matar Shugaban kasar ta janye karar tare da yi wa matashin afuwa.
Sakinsa ke da wuya, ya koma makaranta, inda da ma yake dab da rubuta jarabawarsa ta karshe.