✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya yi yunkurin kashe kansa saboda rashin abinci

Matashin ya ce ya shiga halin matsi tun bayan rasuwar mahaifansa

Wani matashi da ya yi yunkurin kashe kansa a garin Ilorin na Jihar Kwara, Olayinka Segun Owolabi, ya ce tun bayan rasuwar mahaifansa ya fada mawuyacin hali.

Owolabi, wanda dan asalin Jihar Osun ne, ya yi yunkurin rataye kansa da igiya a jikin wata bishiya da safiyar ranar Juma’a, kafin daga bisani a ceto shi.

Bayan ceto shi, an garzaya da shi asibitin Tobi da ke kan titin Taiwo a Ilorin wanda nan take aka ba shi agajin gaggawa.

Bayan gudanar da bincike, matashin ya ce ya gaji da rayuwa bayan ya rasa aikinsa da kuma mahaifansa.

Sannan ya koka kan yadda ya gaza samun agaji wanda abincin da zai ci ma ya ce yana yi masa wahala.

“Wannan shi ne abin da yasa na so na hallaka kaina,” a cewarsa.

Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Ajayi Okasanmi, ya ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar ya ja hankalin matashin game da illar da ke tattare da kisan kai.

Kwamishinan ya ce Ubangiji na fushi da mutanen da ke kashe kansu, kuma laifi ne babba a dokar kasa ga duk wanda ya yi yunkurin aikata hakan.