Wani matashi mai ya yi yunkurin kashe kansa saboda rashin biyan hakkokin mahaifinsa da Gwamnatin Jihar Kuros Riba ta yi, shekara biyar bayan rasuwar mahaifin nasa a bakin aiki.
Matashin mai suna Joseph Odey ya bayyana cewa dadewar ba tare da biyan su hakkin mahaifin nasu ba na iya kai shi ga kashe kansa, saboda halin kuncin rayuwar da suke ciki bayan rasuwar mahaifin nasu.
- ’Yan ta’adda na kokarin kafa sansani a Taraba —Gwamna Darius
- An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa
Ya ce mahaifinsu mai suna Anthony Odey ya yi wa jihar hidima har na tsawon shekara 32 kafin rasuwarsa.
Kafin rasuwar mahaifin nasu, ya kasance Shugaban Makarantar Sakandare ta Ebo da ke Karamar Hukumar Yala a jihar.
A cewarsa, mahaifinsu ya rasu a ranar 12 ga wagan Disamba 2015, shekara uku kafin ya yi ritaya.
“Bayan rasuwarsa, na shiga cuku-cukun takardu don fitowar hakkinsa, a 2017 na kammala komai, a Janairun 2018 kuma aka sahale min.
“Bayan jiran shekara daya ba tare da gwamnati ta biya mu kudin ba, na je wajen Akanta-Janar amma ya ce min babu wasu da za a fitar.
“Ya kara da cewa akwai kudaden wadanda suka yi ritaya tun 2014 da ake jira gwamna ya sa hannu.
“Tun bayan jin haka na ke ta kokarin ganin gwamna ya san halin da ake ciki, amma duk yunkurin da nake yi na gaza cimma nasara.
“Hakkin mahaifina miliyan 13 ne kuma na tabbatar da hakan a ofishin Akanta-Janar.
“Muna fuskantar matsin rayuwa tun bayan rasuwar mahaifinmu, wanda shi ne ke daukar nauyin komai dinmu.
“Kannena mata guda biyu na jami’a kuma suna dab da daina zuwa makaranta, dayar kuma da za ta zana jarabawar WAEC babu tabbacin samun kudin biya mata,” a cewar Odey.
Ya roki gwamnan jihar, Ben Ayade da ya tabbatar da an biya hakkokin ma’aikatan da suka bar aiki don tallafa wa rayuwar iyalansu.
Da yake mayar da martani, sakataren gwamnan kan harkokin yada labarai, Christian Ita, ya ce gwamnatin jihar ta gaji bashin biyan ma’aikata hakkinsu tun 2013.
Ya ce tuni aka kammala biyan ’yan 2013, yanzu kuma suna kan biyan ’yan 2014, wadanda a rukuni-rukuni ake biyan su.