Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wani matashi mai shekara 22, kan zargin safarar tabar Wiwi a Maiduguri.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Nahum Daso Kenneth, ya fitar a Maiduguri, ya bayyana cewa an kama matashin ne a ranar 10 ga watan Janairu, bayan samun sahihan bayanan sirri.
- Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou
- DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato
Jami’an sashen Anti-Squad na ‘yan sanda ne suka kama ɗauke da ƙunshin tabar Wiwi guda 116 a unguwar Zajeri da ke Bolori 2, a Maiduguri.
An miƙa wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka (SCID), domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a kotu.
Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a jihar.
Sannan ta buƙaci iyaye da suke sanya ido sosai kan ’ya’yansu domin kaucewa faɗawa aikata laifi.