Rundunar ’Yan Sandan Bauchi, ta kama wani matashi dan shekara 20 bisa zargin sa da sace wani yaro tare da kashe shi a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis a Bauchi.
- Kisan Sojoji: Basaraken da ake nema ya miƙa kansa ga ’yan sanda
- Addu’a ya kamata Malamai su riƙa yi wa Najeriya ba la’anta ba — Tinubu
Ya ce lamarin ya faru ne a garin Magaman Gumau da ke Karamar Hukumar Toro ta jihar.
Wakil, ya ce rundunar ta samu nasarar cafke matashin da ake zargi da sace yaron mai suna Christopher Bala dan shekara 12.
“Yaron da aka kashe, ɗan wani jami’in ɗan sanda ne mai suna ASP Bala Yarima, mai kula da shiyyar Gumau, a Jihar Bauchi.
“Bayan samun rahoton lamarin, nan take jami’an tsaro daga sashen Toro suka garzaya tare da cafke wanda ake zargin.
“Binciken da muka yi mun gano matashin mai shekara 20 mazaunin Magama Gumau, Rabi’u Adamu, a matsayin wanda ake zargi, suna da alaƙa da yaron da aka kashe,” in ji shi.
Ya kara da cewa a karshe wanda ake zargin ya amsa laifin sace yaron tare da kashe shi, sannan ya amsa karbar Naira 200,000 daga hannun mahaifin yaron a matsayin kudin fansa.
Wakil ya ce, “Ya ji tsoron yaron zai gane shi, shi ya sa ya shaƙe masa wuya har sai da ya mutu, sannan ya tona rami ya birne gawar a ciki,” in ji Wakil.
Kakakin ya ce rundunar ta tono gawar yaron domin tare da kai ta babban asibitin Toro, wanda a nan aka tabbatar da ya mutu ne sakamakon shaƙewa.
Ya ce an miƙa matashin zuwa sashen binciken manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike, bayan umarnin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Auwal Musa ya bayar.
Sai dai kakakin ya yi kira ga iyayen yara da su kasance masu sanya ido kan wadanda ke kulla akala da ‘ya’yansu.