✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya nutse a ruwa yayin ceto saniya a Jigawa

Wani matashi mai kimanin shekaru 18 ya nutse a ruwa a kokarin ceto wata saniyarsa a Karamar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa. Mai magana da…

Wani matashi mai kimanin shekaru 18 ya nutse a ruwa a kokarin ceto wata saniyarsa a Karamar Hukumar Buji ta Jihar Jigawa.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta Sibil Difens reshen Jigawa, CSC Adamu Shehu ne ya tabbatar faruwar lamarin a ranar Lahadi.

Adamu ya ce matashin ya yi gamo da ajalinsa ne a ranar Asabar yayin da daya daga cikin shanunsa biyu da ya kada kiwo ta zame ta fada wani gulbi a birnin Dutse.

“Da ya lura cewa saniyarsa ta fada gulbin, cikin gaggawa ya yi kokarin ceto ta amma ya nutse a ruwan.

“Masu aikin ceto sun tsamo saniyar a raye daga gulbin.

“Sai dai an nemi gawar matashin an rasa sai a ranar Lahadin nan, awa 11 bayan nutsewarsa aka iya gano ta.

“Mun yi bincike kuma mun tabbatar da mutuwar matashin wanda muka mika wa iyayensa gawarsa da a yanzu har an binne shi, a cewar Shehu.